An kashe mutane 30 a hare-haren da aka kai masallatai hudu a Jihar Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Aƙalla mutane 30 ne aka kashe bayan da ’yan ta’adda suka kai hare-hare kan masallatai hudu a ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

Jaridar Blueprint Manhaja ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin gudanar da sallar Juma’a a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana.

Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun mamaye masallatan a lokaci guda, inda suka yi awon gaba da sama da mutum 60 daga cikin masu ibadar. Daga bisani kuma suka tafi da su cikin daji.

Blueprint Manhaja ta ce Shugaban Karamar Hukumar Borgu, Mohammed Nasir Abdullahi, ya tabbatar da cewa kusan mutum 30 daga cikin wadanda aka sace an kashe su.

Ya ce an gano gawarwakin wadanda aka kashe tare da binne su, yayin da jami’an tsaro suka shiga yankin domin bin sawun ’yan ta’addan.

Ya ƙara da cewa wasu gidaje da suka hada da gidan Hakimin Dekara, Abubakar Umar, an kona su yayin harin.

Bayan hare-haren, mazauna yankunan sun fara tserewa zuwa New Bussa da Jamhuriyar Benin saboda barazanar ’yan ta’addan na kashe duk wanda ya ci gaba da zama a yankunan.

Wani mazaunin yankin ya ce mutane kalilan ne suka rage a Dekara, yayin da mafi yawansu suka bar gidajensu domin neman mafaka.

Rundunar ’yansandan Nijeriya ta ce an kaddamar da aikin hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro domin kamo wadanda suka kai harin tare da ceto mutanen da har yanzu suke hannun ’yan ta’addan.

Yawaitar hare-hare a Borgu Mazauna yankin sun ce rashin tsaro ya shafi akalla kananan hukumomi bakwai daga cikin gundumomi 10 na Borgu, lamarin da ya tilasta wa daruruwan mutane, musamman manoma, barin gidajensu.

Sun ce hare-haren sun kuma lalata kauyuka da dama tare da hana manoma zuwa gonakinsu.

A cewar mazauna, tun daga watan Disambar 2025 zuwa Yunin 2026, an kai hare-hare kan kauyuka da dama a yankin, inda aka kashe mutane tare da tilasta wa wasu dubban mazauna yin hijira.

Mazauna sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta Jihar Neja da su kara tsaurara ayyukan tsaro tare da tallafa wa mutanen da suka rasa gidajensu da hanyoyin samun abin dogaro.

Sun kuma bukaci a gudanar da samamen soji domin fatattakar sansanonin ’yan ta’adda da ke amfani da su wajen shirya hare-hare.

By ukarofi

Leave a Reply