Yadda masu tallafa wa ta’addanci ka amfani da asusun bankin mata wajen tura kuɗi — NFIU

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Binciken Bayanai kan Harkokin Kuɗi ta Nijeriya (NFIU) ta gano wata sabuwar hanyar tara kuɗi da ake amfani da ita wajen samar da kuɗaɗe da tura su ga ƙungiyoyin ta’addanci, tare da bayyana wasu dabarun da masu ɗaukar nauyin ta’addanci ke amfani da su wajen ɓoye ainihin waɗanda ke karɓar kuɗin.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa hukumar ta ce masu tallafa wa ta’addanci na buɗe asusun banki da sunayen mata, tare da amfani da lambobin waya wajen harkokin banki ta wayar salula ko karɓar sanarwar mu’amala waɗanda ba a yi wa masu asusun ko ainihin waɗanda ke cin gajiyar asusun rajista ba.

Bayanin na ƙunshe cikin rahoton shekara na NFIU na shekarar 2025, wanda ya bayyana yadda masu taimakawa daga ƙasashen waje, kafafen sada zumunta, asusun wakilai, hanyoyin tura kuɗi da tsarin banki ta wayar salula ake amfani da su wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Rahoton ya ce sabuwar hanyar tara kuɗin ta ƙunshi masu taimakawa daga ƙasashen waje da ke amfani da kafafen sada zumunta wajen neman gudummawa da sunan tallafa wa ayyukan jinƙai ko ilimi, kafin daga bisani a karkatar da kuɗin zuwa ga masu aikata ta’addanci a Nijeriya.

NFIU ta ce ana ƙarfafa daruruwan masu goyon baya su bayar da ƙananan gudummawa, daga dala 50 zuwa dala 500, ta shafukan PayPal ko asusun banki na yau da kullum, domin a guji tayar da hankalin tsarin gano harkokin kuɗin haram.

A cewar rahoton, daga bisani ana tara kuɗin a wani “master account” da wani babban memba na ƙungiyar da ke zaune bisa ƙa’ida a ƙasar waje ke kula da shi.

Bayan kuɗin sun kai wani mataki, ana rarraba su zuwa ƙananan kuɗaɗe da dama, sannan a tura su ta kamfanonin tura kuɗi na ƙasa da ƙasa da manhajojin aika kuɗi zuwa ga wasu mutane a Nijeriya da ake amfani da su wajen karɓa da mika kuɗin.

Hukumar ta ce ɗalibai, ƙananan ’yan kasuwa da ’yan uwa na daga cikin mutanen da ake amfani da su wajen wannan hanya, wadda aka tsara domin guje wa dokokin bayar da rahoton manyan hada-hadar kuɗi tare da ɓoye asalin kuɗin.

NFIU ta ce bayan karɓar kuɗin, ana iya mayar da su tsabar kuɗi, amfani da su wajen sayen abubuwa kamar babura, takin zamani da kayan sadarwar intanet ta tauraron ɗan adam, ko kuma a tura su ta tsarin banki ta wayar salula zuwa ga masu kula da harkokin samar da kayayyaki da masu gudanar da ayyuka a filin daga.

Rahoton ya kuma bayyana amfani da asusun mata a matsayin wakili a matsayin wata sabuwar dabarar ɗaukar nauyin ta’addanci. A wannan yanayin, ana buɗe asusun da sunan mata, yayin da maza masu jagorantar ƙungiyar ko masu kula da kayan aiki ke ɓoye suna sarrafa asusun.

Hukumar ta ce ana amfani da mata saboda wasu al’adun al’umma da ke sa hukumomi ba sa yawan zargin su, inda ake amfani da mata, ’yan’uwa mata ko abokan hulɗa a matsayin abin rufe fuska.

Ta ce a wasu lokuta, mazan ne ke riƙe da katunan ATM, bayanan shiga banki ta wayar salula da lambobin sirri na asusun, yayin da matar da aka yi amfani da sunanta ba ta san irin hada-hadar da ake yi da asusun ba.

NFIU ta kuma bayyana cewa masu tallafa wa ta’addanci na amfani da lambobin waya da ba a yi wa masu asusun ko ainihin waɗanda ke cin gajiyar asusun rajista ba wajen harkokin banki ta wayar salula da karɓar sanarwar mu’amala.

Rahoton ya ce ana amfani da SIM da aka riga aka yi wa rajista, SIM da aka yi wa mutanen da suka rasu rajista, da kuma SIM da ke da alaƙa da asusun da aka buɗe da sunan mata, domin yanke alaƙar da ke tsakanin asusun banki, lambar waya da BɓN.

Hukumar ta ce wannan dabara na iya sa idan aka gano wata mu’amala da ake zargi, masu bincike su bi diddigin lambar wayar zuwa ga wani mutum da ba shi ne ainihin mai aikata laifin ba, yayin da ainihin mai shirya harkar ke ci gaba da kasancewa a ɓoye.

NFIU ta kuma gano cewa wasu ƙungiyoyin ta’addanci na amfani da bayanai ko lambobin sirri a bayanin hada-hadar kuɗi domin ɓoye manufar aika kuɗin da kuma guje wa tsarin bankuna na gano mu’amalolin da ake zargi.

Rahoton ya ce wasu ƙungiyoyin, musamman masu alaƙa da ISWAP, na amfani da cikakkun bayanai a bayanan hada-hadar kuɗi domin kula da tsarin lissafinsu na cikin gida.

Hukumar ta ce wasu masu taimaka musu kuma na amfani da kalmomi marasa ɗaukar hankali, lambobin sirri da wasu haruffa da lambobi wajen bayyana manufar hada-hadar kuɗi, a wasu lokuta kuma suna sauya harshe domin kauce wa matatun kalmomi na bankuna.

Zamba da gibin tsarin fintech sun ƙara tayar da hankali

NFIU ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa barazanar da ake fuskanta na ƙara haɗuwa tsakanin laifukan kuɗi, fasaha da harkokin da suka shafi ƙetare iyakokin ƙasashe.

Ta ce zamba ta ci gaba da kasancewa daga cikin manyan laifukan da ke samar da kuɗaɗe, inda aka samu ƙarin yaɗuwar damfarar Ponzi, damfarar tara kuɗi ta yanar gizo, damfarar saka hannun jari ta hanyar cryptocurrency da kuma zamba da ta shafi kutse cikin asusun sada zumunta da manhajojin aika saƙonni.

Hukumar ta ce waɗannan dabaru na ƙara amfani da gibin da ke cikin tsarin tantance sabbin masu amfani da manhajojin fintech, musamman asusun da ke buƙatar ƙananan bayanan tantance mutum, domin ɗaukar waɗanda za a damfara da kuma tura kuɗaɗe cikin sauri.

Rahoton ya kuma bayyana cewa akwai ci gaba da samun matsaloli a harkokin kula da kuɗaɗen gwamnati, ciki har da karkatar da kuɗaɗen jihohi da ƙananan hukumomi ta asusun jami’an kuɗi da wasu mutane na uku da ke da alaƙa da su.

NFIU ta ce harkokin saye da kwangilolin gwamnati da kuma amfani da tsabar kuɗi na daga cikin wuraren da ke da babban haɗarin almundahana, saboda suna ƙara wahalar bin diddigin yadda kuɗaɗe suka gudana da gano kadarorin da aka samu ta haramtacciyar hanya.

By ukarofi

Leave a Reply