Mauludi: Tinubu ya buƙaci Musulmi su rungumi kyawawan halayen Annabi Muhammad S.A.W

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Maulidin Annabi Muhammad (SAW), inda ya bukace su da su rungumi kyawawan halaye da koyarwar Manzon Allah.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Tinubu ya ce bai kamata bikin Mauludi ya tsaya kan murnar ranar haihuwar Annabi kawai ba, sai dai a yi amfani da lokacin wajen yin nazari, addu’a da koyon darussa daga rayuwarsa.

Ya ce Musulmi su yi kokarin aiwatar da koyarwar Annabi Muhammad, musamman kan ibada, juriya, hakuri, tawali’u da sadaukar da kai.

Shugaban ya kuma buƙaci malaman addini da shugabannin Musulmi su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa Nijeriya addu’a tare da jan hankalin mabiyansu su nuna kishin kasa da kuma amfani da darussan rayuwar Annabi wajen kyautata al’umma.

Tinubu ya kuma yi kira ga masu bikin Mauludi da su taimaka wa mabuƙata da masu rauni, domin nuna tausayi da hadin kai a wannan lokaci.

Haka zalika, ya bukaci a ci gaba da yin addu’o’i domin kawo karshen matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar wasu sassan ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply