Amaechi ya caccaki Sowore kan sukar tsofaffin ’yan siyasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Riɓers kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya caccaki ɗan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, yayin wata mahawara a taron ƙungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) da ke gudana a Fatakwal.

Sowore ya soki ’yan siyasar da suka taɓa riƙe muƙaman gwamnati, yana mai cewa ya kamata su fara bayyana abin da suka cimma a lokacin da suke kan mulki kafin su sake neman shugabanci a zaɓen 2027.

Ya kuma tambayi Amaechi kan ayyukan da ya gudanar a lokacin da yake gwamnan Riɓers da kuma Ministan Sufuri, tare da sukar yadda aka aiwatar da manufofin cire tallafin man fetur.

A nasa martanin, Amaechi ya kare ayyukan da ya ce ya aiwatar a lokacin mulkinsa, ciki har da gina tituna da makarantun firamare a Riɓers, da kuma ayyukan layin dogo a lokacin da yake Ministan Sufuri.

Ya ƙalubalanci Sowore da ya je Riɓers domin ya ga ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar.

“Ina lauyoyin Riɓers? Ku kai Sowore ku nuna masa abin da na yi. Na gina wannan hanya, na gina waccan hanyar, na gina wannan makaranta. Mene ne ƙwarewarka?” inji Amaechi.

Yayin da musayar kalamai ta ƙara zafi, Amaechi ya ce wa Sowore: “Sowore, idan ’yan siyasa suna magana, ka rufe bakinka.” 

Taron karo na 66 na NBA, mai taken “Beyond Limits”, na gudana ne a Fatakwal daga ranar 21 zuwa 28 ga Agusta, inda manyan ’yan siyasa da lauyoyi ke tattaunawa kan shugabanci da makomar Nijeriya gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply