Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Nijeriya ta fara sake tsara harkokin wutar lantarki domin samar da isasshiyar wuta ga masu amfani da ita a cikin ƙasa, tare da samun damar fitar da rarar wutar zuwa kasuwannin ƙasashen Yammacin Afirka, inji Mai Kula da Tsarin Samar da Wutar Lantarki Mai Zaman Kansa na Nijeriya (NISO).
Hakan na zuwa ne yayin da Kamfanin Isar da Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana cewa tsarin layukan wutar lantarkin ƙasar a yanzu na da ƙarfin iya jigilar kusan megawatt 8,700 na wuta.
Manajan Daraktan NISO, Abdu Mohammed, ya shaida wa manema labarai cewa ana mayar da hankali ne wajen inganta tsarin samarwa, isarwa da rarraba wutar lantarki, domin ƙara inganci, jawo jarin masu zuba jari da kuma bai wa Nijeriya damar zama babbar mai fitar da wutar lantarki a yankin Yammacin Afirka.
Ya ce, “Muna sake fasalin kasuwar makamashi, kuma muna da ƙarfin samar da darajar tattalin arziki ga ƙasashen yankin. Muna da ƙarfin da kuma damar samar da makamashin kasuwanci ga maƙwabtanmu.”
Mohammed ya ce NISO na aiki tare da masu ruwa da tsaki a masana’antar wutar lantarki domin inganta haɗin gwiwa tsakanin kamfanonin samar da wuta, tsarin isar da ita da kuma rarrabawa zuwa masu amfani.
Wannan bayani ya zo ne bayan da Ministan Makamashi da Sauyin Tattalin Arziki na Ghana, John Abdulai Jinapor, ya bayyana cewa ƙasarsa na da niyyar faɗaɗa kasuwar fitar da wutar lantarki zuwa Nijeriya.
Ghana a halin yanzu tana fitar da wutar lantarki zuwa Togo, Benin, Cote d’Iɓoire da Burkina Faso, kuma Nijeriya na cikin manyan kasuwannin da take son shiga.
Sai dai Mohammed ya ce babu wata tattaunawa tsakanin Nijeriya da Ghana kan batun shigo da wutar Ghana zuwa Najeriya, yana mai cewa Najeriya tana da isasshen ƙarfin samar da wuta da zai iya biyan buƙatun cikin gida tare da ba ta damar sayar da wutar ga ƙasashen yankin.
Shi ma Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Ababen More Rayuwa na Wutar Lantarki, Sadiƙ Wanka, ya ce Nijeriya da Ghana dukkaninsu mambobi ne na Tsarin Haɗin Kan Wutar Lantarki na Yammacin Afirka (WAPP), wanda ke samar da damar cinikin wutar lantarki tsakanin ƙasashen yankin.
Wanka ya ce Nijeriya na da ɗimbin albarkatun makamashi da suka haɗa da iskar gas, ruwa da hasken rana, sannan ƙarfin da aka girka na samar da wutar lantarki a ƙasar ya fi yawan abin da ake amfani da shi a kan layin ƙasa a halin yanzu.
Ya kuma ƙara da cewa, Nijeriya ta na iya kasancewa mai fitar da wutar lantarki zuwa ƙasashen yankin a nan gaba, ko da yake akwai wasu lokuta da shigo da wutar Ghana zai iya zama mai amfani idan Ghana ta samu rarar wuta a farashi mai sauƙi.
