Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da aka fara yaƙin neman zaɓe a hukumance domin zaɓen shugaban ƙasa da na’yan Majalisar Dokoki ta ƙasa, hankula sun karkata kan yadda ’yan takara za su yi amfani da kafafen yaɗa manufofinsu, domin jan hankalin masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
A halin yanzu, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta tantance ’yan takarar shugaban ƙasa 19 da za su fafata a zaɓen da aka shirya gudanarwa a watan Janairun 2027.
Daga cikin hanyoyin da jam’iyyu da ’yan takara suka saba amfani da su akwai tarukan gangami, shirye-shiryen kai tsaye da na faifan bidiyo, takardun tallace-tallace, fastoci, allunan tallace-tallace, tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai da kuma saƙonnin rediyo.
Rahotanni sun nuna cewa tun kafin a fara kamfen a hukumance, musamman lokacin zaɓukan fidda gwani, garuruwa da ƙauyuka da dama sun fara cika da fastoci da allunan tallata ’yan takara.
Sai dai yayin da wasu hanyoyin kamfen ba su jawo cece-ku ce sosai ba, wasu gwamnatocin jihohi sun sake duba dokokinsu kan allunan talla, lamarin da ya haifar da fargabar cewa ana iya amfani da su wajen takura wa jam’iyyun adawa.
Wasu ’yan siyasa sun bayyana cewa maƙudan kuɗaɗen da aka sanya wa lasisin kafa allunan talla na siyasa ba wai don samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati kawai aka yi su ba, illa kuma ana iya kallonsu a matsayin hanyar tsoratar da ’yan takarar adawa waɗanda ba su da isassun kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe.
Naira miliyan 75 kan allon tallan ɗan takarar shugaban ƙasa a Ribas:
A Jihar Ribas, gwamnati ta sanya Naira miliyan 75 a matsayin kuɗin lasisin kafa allon tallan ɗan takarar shugaban ƙasa, yayin da na ɗan takarar gwamna yake Naira miliyan 50.
Wata majiya daga ofishin mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa ta ce an sanya kuɗin ne domin daƙile yawaitar kafa allunan talla ba bisa ƙa’ida ba a Fatakwal, babban birnin jihar.
A ƙaramar hukumar Abua/Odual kuwa, an sanya Naira miliyan 70 ga ’yan takarar shugaban ƙasa da Naira miliyan 50 ga ’yan takarar gwamna.
Majalisar Dokokin ƙaramar Hukumar Abua/Odual ta kuma amince da wata sabuwar ƙa’ida da ta tanadi lasisi kafin a kafa fastoci, banners, allunan talla da sauran kayan yaƙin neman zaɓe a wuraren jama’a.
A ƙarƙashin tsarin, ɗan takarar shugaban ƙasa zai biya Naira miliyan 75, gwamna Naira miliyan 50, Sanata Naira miliyan 30, ɗan Majalisar Wakilai Naira miliyan 20, ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukuma Naira miliyan 15, ɗan Majalisar Dokokin Jiha Naira miliyan 10, yayin da ɗan takarar kansila zai biya Naira miliyan ɗaya.
Kano ta fi sassauci:
A Kano kuwa, kuɗin ya yi matuƙar sauƙi idan aka kwatanta da wasu jihohi. Hukumar Alamomi da Tallace-tallace ta Jihar Kano, ta ce a halin yanzu ba ta bambanta allunan tallan siyasa da na kasuwanci ba.
Daraktan Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Munzali Muhammad Hausawa, ya ce hukumar tana aiki ne da kamfanonin talla da aka yi wa rajista a Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Nijeriya (APCON).
A cewarsa, ɗan siyasa zai tuntuɓi kamfanin talla, wanda zai biya kuɗin gudanarwa da na shekara, wanda jimillarsa ta kai kusan Naira miliyan 1.15.
Kogi ta sanya Naira miliyan 150 ga ‘yan takarar shugaban ƙasa:
A Jihar Kogi kuma, gwamnati ta amince da Naira miliyan 150 a matsayin kuɗin tallan ɗan takarar shugaban ƙasa. Sanata zai biya Naira miliyan 50, ɗan Majalisar Wakilai Naira miliyan 30, yayin da ɗan Majalisar Dokokin Jiha zai biya Naira miliyan biyar.
Haka kuma, an sanya Naira miliyan biyu ga ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukuma da Naira 300,000 ga ɗan takarar kansila.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce duk wanda ya kafa kayan kamfen ba tare da biyan kuɗin da aka tanada ba zai fuskanci hukunci.
Sai dai Jam’iyyar PDP a jihar ta yi watsi da kuɗaɗen, tana mai cewa sun yi yawa kuma suna iya zama wata dabara ta toshe hanyar ’yan adawa.
Shugaban PDP na Kogi, Mohammed Gambo, ya ce gwamnati tana da ikon tsara yadda ake amfani da wuraren tallace-tallace, amma bai kamata dokar ta zama wani shinge na kuɗi da zai hana ’yan takara bayyana manufofinsu ga jama’a ba.
A Kaduna kuwa, babu wani ƙayyadadden kuɗi guda da aka bayyana. Hukumar Kula da Gine-gine da Tsari Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA) ta ce mai son kafa allo zai fara nuna wurin da yake son amfani da shi, sannan hukumar ta tantance wurin ta sanya kuɗin da ya dace.
A Bauchi kuma, hukumomin jihar sun bayar da umarnin cire allunan talla, banners da fastocin kamfen da aka kafa a kan fitilun titi, sandunan amfani da jama’a da manyan gadar sama.
Sai dai Jam’iyyar PRP ta zargi gwamnati da aiwatar da dokar ba bisa adalci ba, tana cewa kayan kamfen na wasu jam’iyyu sun ci gaba da kasancewa a wuraren jama’a.
A Abia, ɗan takarar shugaban ƙasa zai biya Naira miliyan 200, gwamna Naira miliyan 150, Sanata Naira miliyan 100, ɗan Majalisar Wakilai Naira miliyan 50, yayin da ɗan Majalisar Dokokin Jiha zai biya Naira miliyan 20.
A Anambra, kuɗin shugaban ƙasa ya kai Naira miliyan 50, Sanata Naira miliyan 20, Majalisar Wakilai Naira miliyan biyar, Majalisar Dokokin Jiha Naira miliyan 1.5, shugabancin ƙaramar hukuma Naira miliyan 2.5, kansila kuma Naira 100,000.
A Kuros Riba, shugaban ƙasa zai biya Naira miliyan 150, gwamna Naira miliyan 100. A Enugu kuma an bayar da rahoton cewa an sanya Naira miliyan 150 kafin ’yan takara su kafa allunan talla, amfani da motocin kamfen masu tambari ko yaɗa wasu kayan kamfen.
Jam’iyyun adawa sun yi tir:
ADC ta ce za ta ƙalubalanci irin waɗannan kuɗaɗe a kotu, tana zargin cewa ana amfani da su wajen takura wa ’yan adawa.
Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar na aasa, Bolaji Abdullahi, ya ce matakin “a fili yake an nufi ’yan adawa da shi.”
Haka kuma, NDC ta soki abin da ta kira ƙarin kuɗaɗen da ba su dace ba, tana cewa hakan na iya raunana fafatawar siyasa.
Masana sun nuna damuwa:
Masanin kimiyyar siyasa na Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fage, ya ce sanya irin waɗannan kuɗaɗe a lokacin da zaɓe ke gabatowa na iya zama abin damuwa.
A cewarsa, ko da gwamnati na ikirarin neman kuɗaɗen shiga ne, akwai haɗarin amfani da tsarin wajen takura wa jam’iyyun adawa.
Ya ce dimokuraɗiyya tana buƙatar filin fafatawa da ya kasance daidai ga kowa, domin kada jam’iyya mai mulki ta samu damar yin abin da ’yan adawa ba za su iya yi ba saboda tsadar kuɗi.
Wani mai fafutukar ci gaban matasa, Olasupo Abideen, shi ma ya ce ya dace a binciki dalilin da ya sa aka bullo da irin waɗannan kuɗaɗe a wannan lokaci, da kuma ko an yi shawarwari da jam’iyyun siyasa kafin aiwatar da su.
Daraktan Media Adɓocacy and Technologies Centre (MATEC), Musa Aliyu, ya ce kuɗaɗen allunan talla na iya zama halastacciyar hanyar samun kuɗin shiga, amma bai kamata neman kuɗaɗen shiga ya lalata daidaiton fafatawar siyasa ba.
APC ta ce ba ta da hannu:
Jam’iyyar APC ta ce ba ta da hannu wajen ƙayyade kuɗaɗen. Wani jigo a jam’iyyar ya bayyana cewa jihohi da ƙananan hukumomi ne ke da ikon sanya irin waɗannan kuɗaɗe.
Ya ce matsalar za ta taso ne idan an hana ɗan takara kafa allon talla duk da ya biya kuɗin da aka tanada.
Sabon dokar zaɓe ta ƙara iyakar kuɗin kamfen:
A wani muhimmin sauyi, Dokar Zaɓe ta 2026 ta ninka iyakar kuɗin da ɗan takarar shugaban ƙasa zai iya kashewa daga Naira biliyan biyar zuwa Naira biliyan 10.
Ga ɗan takarar gwamna, iyakar ta tashi daga Naira biliyan ɗaya zuwa Naira biliyan uku. Sanata zai iya kashe har Naira miliyan 500, daga Naira miliyan 100 a dokar 2022, yayin da ɗan Majalisar Wakilai zai iya kashe Naira miliyan 250, daga Naira miliyan 70.
Ga ɗan Majalisar Dokokin Jiha, iyakar ta tashi daga Naira miliyan 30 zuwa Naira miliyan 100. Shugaban majalisar ƙaramar hukuma zai iya kashe Naira miliyan 100, kansila kuma Naira miliyan 10.
Sai dai wani lauya mai ƙwarewa kan kundin tsarin mulki, Kehinde Oloje, ya ce Dokar Zaɓe ba ta tanadi takamaiman kuɗin kafa allunan talla ba. A cewarsa, jihohi da ƙananan hukumomi ne ke tsara wannan batu ta hanyar dokokin tsara birane da hukumomin kula da alamomi da tallace-tallace.
Ya ce duk da haka, dokar zaɓe tana tsara lokacin kamfen da irin saƙonnin da za a yaɗa, tare da hana kamfen a kusa da rumfunan zaɓe da kuma hana tallan siyasa a cikin sa’o’i 24 kafin zaɓe.
A ƙarshe, yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, tsadar allunan talla na iya zama wani sabon babban ƙalubale ga ’yan takara, musamman jam’iyyun da ba su da ƙarfin kuɗi. Masu sharhi na ganin cewa duk da halaccin gwamnati na tsara tallace-tallace da samar da kuɗaɗen shiga, bai kamata wannan iko ya zama hanyar rage damar ’yan siyasa na isar da saƙonsu ga masu zaɓe ba.
