05
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA A halin da ake ciki, birnin tarayya, Abuja da jihar Legas da River da kuma Oyo, su ne jihohin da ke kan gaba wajen samun mafi yawan waɗanda suka harbu da cutar korona a tsakanin sa'o'i 24 da suka gabata. Bayanan Cibiyar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), sun nuna an samu ƙarin mutum 1,340 da suka kamu da cutar korona. Ƙarin da cibiyar ta ce ya shafi wasu jihohin ƙasar nan su 22, ciki har da Abuja 320, Lagos 275, Rivers 117, da kuma Oyo 100. Sauran sun haɗa da Sakkwato 3, Kaduna 31, Katsina 14,…
