Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ɗan Takarar Shugabancin ƙasa na Jam’iyyar Accord, Dakta Gbenga Olawepo-Hashim, ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar PDP a zamanin mulkin tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo sun yi watsi da yunƙurin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na cire tallafin man fetur.
Olawepo-Hashim ya ce ra’ayin Atiku na cire tallafin mai ya samo asali tun kafin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan farko da suka fara fafutukar ganin an cire tallafin man fetur tare da mayar da kamfanonin gwamnati gaba ɗaya hannun masu zaman kansu a Jamhuriyar Tarayya ta Huɗu.
Ya tuna cewa a shekarar 1999, a lokacin gwamnatin Obasanjo, lokacin da Atiku yake Mataimakin Shugaban ƙasa kuma yake jagorantar tawagar tattalin arzikin gwamnati, gwamnatin ta ƙara farashin kayayyakin man fetur tare da cire tallafin.
Olawepo-Hashim ya kira Atiku “uban cire tallafin mai” a Jamhuriyar Tarayya ta Hudu, yana mai cewa sauyin matsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi a yanzu game da cire tallafin na buƙatar ya yi wa ’yan Nijeriya bayani tare da neman afuwa.
Ya ce, “Gaskiyar magana ita ce, kafin Tinubu ya shigo fagen siyasar ƙasa, Atiku shi ne uban ra’ayin cire tallafin mai da kuma mayar da harkokin gwamnati gaba ɗaya ga kamfanoni masu zaman kansu a wannan Jamhuriya. Shi da tawagar tattalin arzikinsa ne suka jagoranci wannan ra’ayi.
“Mun yi musu tsayin daka sosai a farkon gwamnatin Obasanjo.”
Olawepo-Hashim ya ce shi da wasu jami’an PDP sun fito fili suka yi adawa da ƙarin farashin man fetur da kuma cire tallafin da gwamnatin Obasanjo ke son aiwatarwa, a lokacin da Atiku ke jagorantar tawagar tattalin arzikin gwamnatin. Ya ce Iro Dan Musa, wanda a lokacin shi ne Mataimakin Shugaban PDP na ƙasa; Harry Marshall, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Yankin Kudu maso Kudu; Abubakar Magaji, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya; Emmanuel Ibeshi, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa; da shi kansa, wanda a lokacin yake Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa, sun gudanar da taron manema labarai tare, inda suka yi Allah-wadai da ƙarin farashin man fetur da cire tallafin.
Ya ƙara da cewa, Majalisar Dokoki ta ƙasa ita ma ta zartar da wasu ƙudurori na adawa da manufar, abin da daga bisani ya sa ɓangaren zartarwa ya janye matakin. “Mun yi adawa da cire tallafin a lokacin da yin hakan bai da wani amfani a siyasa. Ba wai yanzu ne kawai muka gano wahalar da ’yan Nijeriya ke ciki saboda wata sabuwar zaɓe ta matso ba,” inji shi.
Ya ce tarihin abin da ya faru ya tabbatar da cewa adawarsa da cire tallafin ba wata dabara ce ta neman ƙuri’a ba. Olawepo-Hashim ya ce a tsawon lokaci yana adawa da cire tallafin man fetur, inda ya sake nanata matsayarsa a wata hira da Trust Tɓ a makon da ya gabata. A cewarsa, ya kamata a dawo da tallafin man fetur da wasu muhimman kayayyaki domin kare ’yan ƙasa da kuma sassan tattalin arzikin da ke samar da kaya daga mummunan tasirin tashin farashi.
Ya ce sauyin matsayar wasu ’yan siyasa da suka taɓa goyon bayan cire tallafin yana haifar da tambayoyi kan sahihancin sabbin matsayinsu. “Wasu ’yan takara da suka yi kamfen a zaɓen da ya gabata domin cire tallafin, yanzu suna sauya matsayarsu ba tare da sun nuna nadama kan jahilci da rashin tausayin da suka nuna wa jama’a a baya ba,” inji shi.
Musamman ya soki Atiku kan sauya matsayarsa ba tare da ya amince da irin rawar da ya taka a baya wajen goyon bayan cire tallafin ba.
