Buhari ya tsawaita shekarun ritaya ga malamai a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar tsawaita shekarun ritayar malamai a Nijeriya.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

A ranar 20 ga Janairu, 2021, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da wani ƙudirin doka da ke neman ƙara shekarun yin ritaya da kuma shekarun hidimar malamai.

Jigon ƙudirin dokar dai shi ne bayar da goyon baya a shari’a don amincewa da sabon shekaru 65 na ritaya daga shekaru 60 ga malaman da kuma tsawaita wa’adin aikinsu daga shekaru 35 zuwa 40, inji Ministan Ilimi, Adamu Adamu.

A cewar Ministan, ƙudirin ya kuma buƙaci gabatar da alawus-alawus na canjin wuraren aiki na musamman a karkara, da sauran abubuwa da za su ƙarfafa gwiwar haziƙan ’yan Nijeriya su rungumi aikin koyarwa.

Bayan miƙa ta ga majalisar dokokin ƙasar bayan ‘yan watanni, ‘yan majalisar wakilai a majalisar sun amince da ƙudirin a ranar 9 ga watan Nuwamban bara.

Yanzu haka dai malamai a faɗin ƙasar sun ƙara wa’adin ritayarsu da kuma shekarun aikinsu da shekaru biyar yayin da shugaba Buhari ya amince da dokar da ta dace da shekarun ritayar malamai a Nijeriya.