Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus

Daga BASHIR ISAH

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi murabus daga matsayin sanata mai wakiltar shiyyar Nasarawa ta yamma a jihar Nasarawa.

Haka shi ma mataimakinsa na Arewa, Abubakar Kyari, ya yi murabus a matsayin sanata mai wakiltar Borno ta Arewa.

A yau Talata Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta wasiƙun ajiye muƙaman sanatocin biyu yayin zaman majalisar.

Waɗanda lamarin ya shafa sun ajiye muƙaman nasu ne biyo bayan nasarar da suka samu na zama shugabannin jam’iyyarsu ta APC a matakin ƙasa.

Kafin wannan lokaci, Sanata Adamu shi ne shugaban kwamitin harkokin noma da raya karkara na Majalisar Tarayya.

A cikin wasiƙar da ya aika wa majalisa, Adamu ya ce wasiƙar sanarwa ce a hukumance dangane da ajiye muƙaminsa na sanata wanda ya soma aiki daga ranar 1 ga Afrilun 2022.

Kazalika, Sanata Adamu ya nuna godiyarsa game da irin goyon baya da haɗin kan da ya samu daga wajen takwarorinsa a iya zaman da ya yi a majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *