‘Yan daba sun kashe wani malamin jami’a a Jos

Daga HABU ƊAN SARKI

Wasu yara matasa ɗauke da makamai sun kashe wani malamin Jami’ar Tarayya da ke Gashua a Jihar Yobe, Muhammad Sani Mazadu, ta hanyar harbin sa da bindiga, yayin wani rikicin ýan daba a Anguwar Rogo da ke cikin garin Jos, ranar Litinin da maraice daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke buɗa bakin azumin Ramadan na goma da suka kai.

Rahotanni sun bayyana cewa, marigayin wanda magidanci ne da ke da yara uku, ya rasu ne a Babban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), inda aka garzaya da shi, don ceton ransa daga harbin harsashin da aka yi masa.

A wani rubutu da ya yi a shafin sa na fesbuk, ɗan uwan marigayin wanda kuma kwamishina ne a Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, Yusha’u Mazadu, ya tabbatar da rasuwar ɗan uwan nasa tare da yi masa addu’ar ubangiji Allah ya sa aljanna ce makomar sa.

Hukumar gudanarwar Jami’ar Tarayya da ke Gashua ta hannun shugaban sashin kula da watsa labarai na jami’ar Adamu Saleh ya bayyana alhininta da jajenta ga iyalin marigayin, wanda ta bayyana cewar kafin rasuwar sa marigayin malami ne da ke koyar da ilimin halayyar ɗan Adam.

Wannan mummunar halayya ta ɓatagarin matasa da ke shigowa cikin anguwa suna sare sare da harbe harbe da makami ya daɗe yana ci wa masu faɗa a ji a cikin garin Jos tuwo a ƙwarya, duk da yanayin da ake ciki na ibada a wata mai tsarki.

Tuni dai wasu shugabannin al’umma irin su shugaban Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa Shehu Bala Usman da Alhaji Sani Mu’azu da shugaban ƙungiyar matasa Musulmi ta ƙasa NACOMYO, Alhaji Sani Suleiman da sauran magabata suka yi Allah wadai da wannan ɗanyen aiki da matasan ke neman dawo da shi cikin garin Jos, bayan yaƙin da aka yi a baya, abin ya soma sauƙi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar, ya yi kira ga jami’an tsaro su tabbatar sun ɗauki mataki a kai da gurfanar da masu hannu a wannan ɗanyen aikin gaban hukuma, tare da alƙawarin cigaba da tallafawa ƙungiyoyin ýan banga da sauran jami’an tsaro, don kawo ƙarshen wannan tsageranci a faɗin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Gwamnatin Jihar Filato dai na cikin wani hali na tsaka mai wuya a ýan makonnin nan, sakamakon ƙaruwar taɓarɓarewar tsaro a sassan jihar, da ke da nasaba da hare haren ýan bindiga da faɗan ƙabilanci a ƙananan hukumomin Bassa, Kanam da Wase, inda ko a ƙarshen makon da ya gabata ma sai da wasu ýan bindiga suka kashe mutane fiye da 130 a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Kanam.