Harin Filato: Tilas maharan su fuskanci hukunci – Buhari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne maharan da suka kai mummunan hari a ƙauyukan Kanam da Wase a jihar Filato su fuskanci hukuncin abin da suka aikata, tare da bayyana harin a matsayin ƙololuwar ƙeta ga jama’a.

Mai Magana da Yawun Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya bayar a ranar Talata.

Shehu ya ce, Buhari ya bada umarnin “Kada a sassauta musu, kuma babu yafiya.”

KARANTA: INEC ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau sama da miliyan 1.3

Ya ƙara da cewa, Buhari ya umurci hukumomin da lamarin ya shafa da su haɗa kai su yi aiki tare da gwamnatin jihar Filato don tabbatar da an zaƙulo dukkan masu hannu a harin don doka ta yi aikinta.

Buhari ya yi amfani da wannan dmaa wajen miƙa ta’aziyyarsa ga ahalin waɗanda aka kashe a harin, kana ya bada tabbacin cewa tilas a maido da zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *