Gidauniyar IDDEF ta aza harsashin gina kwalejin ilimi a Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A ƙoƙarin da ta ke yi na samar da ilimi da bunƙasarsa a ƙasashen Musulmi na duniya, Gidauniyar ‘Insana Deger Veren Demekler Foundation’ wato IDDEF a ƙarƙashin Cibiyar Bincike da Samar da Ilimi ta Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, wato ‘Sheikh Muhammad Nasiru Kabara Research Center’, ta ƙaddamar da bikin aza harsashin gina kwalejin ilimi mai suna ‘Sheikh Muhammad Ifandi International College’ domin samar da ingantaccen ilimin addini da na zamani a tsakanin al’ummar Musulmi da ke Jihar Kano da sauran wasu yankuna da ke kusa da ita.

Taron wanda aka gudanar a ranar Asabar ɗin makon jiya wato 26/3/2022 a ƙauyen Burungawa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ya samu halartar Shugaban Gidauniyar IDDEF ɗin na duniya, Sheikh Muhammad Turan wanda ya zo daga ƙasar Turkiyya tare da sauran manyan malamai.

Tun da farko da ya ke Jawabi a wajen taron, Babban mai kula da Gidauniyar IDDEF a Nijeriya, Malam Asikiya Sheikh Muhammad Nasiru Kabara ya bayyana cewa, “kamar yadda aka saba wannan Gidauniyar kullum cikin gudanar da ayyukan cigaba da raya al’umma take.

KARANTA: Wakilan ɗaurarrun sheɗanu a watan Ramadan

“Kuma a wannan lokaci ma  abin da muka taru mu gudanar kenan wato bikin aza harsashin makarantar kwaleji da za a yi domin cigaban ilimin addinin Muslumci a Nijeriya, kuma a wannan waje da za a gina wannan makaranta, sunan sa Darruz Zikri wanda Maulana Amiril Jaishi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara ya sanyya masa sunan, kuma nan ce mahaifarsa cibiyarsa tana nan wajen da za a gina wannan makaranta, kuma daman wannan waje gona ce ta sa wacce muka gaje ta muka ga ya dace mu sadaukar da ita a gina makaranta, domin ya rinqa samun lada a kan wannan aikin alheri da ya dasa ya tafi ya bari”.

Ya ƙara da cewa, “duk da yanayin lokaci, amma za mu so a ce an kammala aikin daga nan zuwa watanni 6, don fatan mu a gama a kan lokaci jama’a su fara amfana daga irin alhairan da wannan makaranta ta ƙunsa, domin makaranta ce da za ta samar da ilimi nagartacce, na addinin Muslumci da kuma na zamantakewar rayuwar yau da kullum, kamar abin da ya shafi haddar Ƙur’ani da Hadisi da Tajwidi da Kimiyya da sauran fannoni ilimi na rayuwa, amma dai tashin farko muna son mu fara da ajujuwa guda 8 wanda kowanne aji muna sa ran zai ɗauki mutum 25 zuwa 30.”

Shi ma da ya ke Jawabi a wajen. Shugaban Gidauniyar ta IDDEF na duniya, Sheikh Muhammad Turan ya nuna farin cikinsa da zuwa sa garin kano daga ƙasar Turkiyya domin halartar taron, domin a cewarsa zuwan na sa ya sa ya haɗu da ‘yan uwa Musulmi wanda kuma hakan ya saka shi farin ciki sosai, don haka ya yi kira da al’ummar Musulmi su rungumi ɗabi’ar haɗin Kai da zaman lafiya domin samar da cigaban da a ke buƙata a ƙasashen Musulmi.

Daga ƙarshe ya yi alwashin bayar da duk wata gudummawar da ta kamata domin samun ci gaban makarantar da sauran abubuwan da Gidauniyar ta IDDEF ta ke gudanarwa a Nijeriya da duniya baki ɗaya.