Wakilan ɗaurarrun sheɗanu a watan Ramadan

Ba wannan ne karo na farko ba, amma wannan ne karo na farko da abun ya ke dawo min a tunani na, kan yanda na ke kallon lamarin a duk farkon wannan wata Ramadan mai daraja.

Da ni, da kai da mu da ke, da su, duka iya waɗanda ke kallon gabas, domin yin sallah da salati, mun daɗe tun tasowar mu da sanin wani hadisi; wanda ko dai mu ka koya a Islamiyya ko kuma mu ka jiyo a bakin Malamai, kan cewar, duk lokacin da azumin watan Ramadan ya kama, ana buɗe kofofin Aljanna a kuma rufe na wuta sannan ana ɗaure aljanu da shaiɗanu. Hikimar hakan, abu ne da saninsa ya ɗarsu a tunanin kowane mumini mai imani.

Ramadhan wata ne mai daraja, mai falala, watan azumi, watan sallah da nafila. Wata ne da za mu kira da watan garaɓasa mai ƙunshe da kwanaki da lokuta masu ɗimbin alfanun da ake farautar gwaggwavar ladar neman kusanci ga Allah buwayi, bisa doron ladubban siffanta kai da kyawawan ayyuka a duk kan janibin rayuwar mu ta yau da kullum.

Haka nan wata ne da ke da wa’adin farawa da ƙarewa, wannan ya sa duk kan abun da za ka yi a cikin sa (na ibada) ladan sa kan ninku saɓanin in ba a watan ba ne. Mai Azumi ana Son ya cusawa kan sa (ko da ba haka ya ke ba kamin azumin) halaye da ɗabi’u nagari, tare da yin hannun riga dama nisantar duk wani abu da ya ke yi na akasin hakan.

Kalmar Musulunci akan duk wani abun halitta ita kaɗai, ba za ta zamo masa tsanin kai wa ga rahamar Allah ba, sai ya zama mai bi da kuma kare dokokin Allah cikin duk wani fasali na umurni da kuma hani da aka yi masa cikin tafarfarar ƙa’idojin shari’ar addinin Islama da ya ke amsa sunan ɗan cikinsa.

Ba ƙaramin taƙadiranci, sheɗanci, tsageranci da kuma rasar kunya bane mutum, ya kasance da wani hali na banza matuqa, a baɗinin sa, kuma ya fito sarari ya na bayyanar da shi ba, sai dai in dama imani ya ƙauracewa ƙoƙon zuciyarsa.

An kama shaiɗanu da Aljanu an ɗaure, amma mu kuma gamu da wakilan su acikin al’ummar mu a yau. Sun zama jakadun su, su na nan a cikin gidajen mu, maƙotan mu, unguwanni dama yankin mu gabaɗaya.

Sai dai ya kamata mu san da cewar wanda ya ɗaure aljanu da shaiɗanun nan fa ba shi zai sauqo ya ɗaure mana su (Miyagun Mata) ba fa.

Manzon Allah (S.A.W.) Ya yi gaskiya. A ma’anar wani hadisi, cikin  ruwayoyin Bukhari da Muslim, ya bayyana cewa, bai bar wata fitina ba ga maza (bayan sa) face mata.

Wallahi iyaye ya kamata ku ji tsoron Allah. Ke Hajiya Wance da Mallam Wane, waɗannan ‘ya’ya matan da ka ke da iko a kan su, ko su ke gaban ka idan har sun daina ci da sha, sun lazimci yin Sallah lokuta 5 ɗin nan, wannan hakkin Allah ne a kan su kai-tsaye. Ku kuma (Iyaye) da su ke fita a gaban ku, ku ke zaune a da su a gida guda, hakkin Allah ne a kan ku, kan ku lura da irin yanayin shigar da su ke yi.

Duk lokacin da ka ga ‘yar musulma a titi da shiga mai tayar da hankalin nan, kar ka fara kawo komai sai sakacin iyaye. Damar da ku (iyaye) ke baiwa ƴaƴan ku (mata) na yin shigar da duk su ka ga dama a matsayin su na ƴan mata ne ko zawarawa, bisa manufar ita kaɗaice hanyar da namiji zai gan su ya ƙyasa, ita ce mafarin ƙofar halakar da ku ke buɗe musu. Har ta kai ga daga yin abun da ku ke bin son zukatan ku wajen son ayi, har kuma a samu zurmuƙen zuwa kan abun da ba kwa so kuma ba ku yi tsammani za a yi ba. 

Wai a tunani irin na Ahmad Nagudu, nasiha ce gare ku (Iyaye) a nan, ba Sallah da Salati da tsayuwar dare da nafilfili da sadaka gami da ciyarwa kaɗai ya kamata ku takaita ba, kamata ya yi ku faɗaɗa wajen taya Allah kiwo ta hanyar kame ƴaƴan ku mata ku ɗaure (hana su shigar banza) kamar yadda aka ɗaure shaiɗanun mutanen ɓoye, don kaucewa barin ƴaƴan ku su kasance jakadun Iblis a ban ƙasa cikin wannan wata mai albarka.

Ahmad Nagudu ya rubuto ne daga Kano. – 08098638510