Labarai

UEFA ta ɗauki matakin shari’a kan FIFA da Infantino

Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) na shirin ƙaddamar da shari'a a ƙasar Switzerland kan shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-ƙasa (FIFA), Gianni Infantino da wasu jami’an hukumar. Batun ya samo asali ne daga wani shirin FIFA da aka yi watsi da shi na siyar da kaso 20 na haƙƙin kasuwancin gasar cin kofin duniya da wasu gasa ga masu zuba jari masu zaman kansu kan Dala biliyan 4.2. UEFA na zargin cewa an tsara shirin ba tare da cikakken bin tsarin gudanar da FIFA ba, kuma tana son samun wasu takardu da shaidu daga hukumomin FIFA da…
Read More

TCN ya yi wa AEDC martani kan dalilan rashin samun wadataccen lantarki a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa TCN, ya bayyana kalaman Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) a matsayin kuskure kuma abin ruɗarwa, inda AEDC ya danganta rage matakin raba wuta da zargin rage ƙarfin layukan lantarki daga tashar wuta ta Shiroro. A wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, TCN ya ce rage adadin lantarkin ga AEDC ya faru ne sakamakon ƙarancinsa daga rumbun lantarki na ƙasa, ba wai daga layukan tashar Shiroro ba kamar yadda AEDC ta yi iƙirari. Da fari dai AEDC ya fitar da wata sanarwa, inda a…
Read More
‘Yan sanda sun kama mutum biyu da zargin taimakon ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da zargin taimakon ‘yan bindiga a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda da haɗin gwiwan 'yan banga sun kama mutane biyu da ake zargi da taimakawa yan bindiga a ƙaramar hukumar Jibiya. A wata sanarwa jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa sanda suka tare wata Mota ƙirar Volkswagen Golf numba TFA 29 AA. A bincike da suka gudanar sun gano direban motar mai suna Babangida Mohammed Yana ɗauke da wani mai suna Rabi'u Isah da wasu kaya da ake zargi za su kaiwa 'yan bindiga a nan Jibiya. DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa…
Read More

Ɗan Shugaban Uganda na shirin maye gurbin mahaifinsa bayan sama da shekara 40 a muƙamin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban rundunar sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, wanda shi ne ɗan Shugaba mafi daɗewa kan karagar mulkin ƙasar, Yoweri Museveni, ya bayyana aniyarsa ta fitowa takara a zaɓen 2031 na ƙasar, lamarin da ke nuna yana son zama magajin mahaifin nasa a muƙamin. Kainerugaba mai shekaru 52 ya yi wannan iƙirari ne a wasu wallafe-wallafe da aka yi a kafar X, ranar Talata. Hakan na zuwa ne bayan sama da shekaru 40 da mahaifinsa ke jagorantar ragamar siyasar ƙasar. "Zan nemi takarar babban ofishin ƙasar a 2031. Kuma za mu yi nasara da yardar Ubangiji…
Read More

Shugaban ƙasar Guinea ya sallami sojoji 173

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Janar Mamadi Doumbouya na Guinea, ya sallami dakarun sojin ƙasar guda 173 daga aiki bisa zargin barin wajen ayyukansu ba tare da izini ba. Gidan talabijin na ƙasar ne ya sanar da matakin a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2026. Janar Amara Camara, wato Sakataren gwamnatin mulkin sojin ƙasar ne ya sanar da matakin a madadin fadar Shugaban ƙasar. Daga cikin waɗanda matakin ya shafa akwai Kwamanda Michel Lamah, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jami’an rundunar Forces Spéciales, kuma ya taka rawa a juyin mulkin da ya hamɓarar da tsohon Shugaba,…
Read More

Tinubu ya umarci a yi gagarumin gyara ga harkar ƙwallon ƙafa a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci da a gudanar da gagarumin gyara a fannin harkokin ƙwallon ƙafan Nijeriya domin shawo kan matsalolin rashin nasara da tawagogin 'yan wasa suka fuskanta a gasan matakan nahiya da na duniya. Ya ce, wajibi ne gyaran ya ƙunshi ƙarfafa harkar shugabanci, gudanarwa, wakilcin masu ruwa da tsaki, ci-gaban damarmaki, wasannin gida da tabbatar da gaskiya da adalci a harkar ƙwallon Nijeriya. Shugaban ya bayyana cewa, yayin da wasu wasanni suke samun nasarori tun bayan sake kafa Hukumar kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC), harkar ƙwallon na cigaba da fuskantar…
Read More

Tinubu ya rantsar da Abel Enitan a matsayin Shugaban Ma’aikatan Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Mista Abel Enitan Olumuyiwa a matsayin sabon Shugaban Ma'aikatar Ma'aikatan Tarayya (HoCSF). Enitan ya maye gurbin Misis Didi Esther Walson-Jack, wadda ta yi ritaya bayan cimma shekarun yin ritaya na 60. An gudanar da ƙaramin taron rantsuwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, lamarin da ya yi sanadin fara wa'adin Enitan a matsayin shugaban ma'aikatan Nijeriya. A ranar 19 ga Agusta ne Tinubu ya naɗa Enitan a muƙamin, a matsayinsa na mafi girma cikin manyan sakatarorin ma'aikatun tarayya. Waɗanda suka halarci taron sun…
Read More

Emmanuel Ikpeme ya zama babban sakataren NFF na riƙo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa NFF, ta kira taron gaggawa a Abuja bayan murabus ɗin Shugabanta Ibrahim Gusau da 'yan kwamitin zartarwarsa a ranar Alhamis bayan matsi daga Hukumar kula da Harkokin Wasanni ta Ƙasa (NSC). Majiyoyi sun ce akwai yiwuwar a soke gudanar da zaɓen NFF da aka shirya a 27 ga Satumba, 2026 a Lafia, Jihar Nasarawa, da samar da wani kwamiti da zai jagoranci gudanar da harkokin hukumar har zuwa lokacin da za a yi sabon zaɓe. Bayan murabus ɗin Babban Sakataren, Dakta Mohammed Sanusi a ranar Alhamis, mataimakinsa, Dakta Emmanuel…
Read More
An gano gawarwaki mutum 30 bayan harin ’yan ta’adda kan masallatai a Neja – Shugaban Borgu

An gano gawarwaki mutum 30 bayan harin ’yan ta’adda kan masallatai a Neja – Shugaban Borgu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kimanin mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai wa masu ibada a lokacin sallar Juma’a a ƙananan hukumomin Borgu na Jihar Neja, yayin da aka yi awon gaba da sama da mutum 60, a cewar Shugaban Ƙƙaramar Hukumar Borgu, Mohammed Abdullahi. Abdullahi ya ce, maharan sun sace sama da mutum 60 daga masallatai daban-daban a ƙauyuka huɗu, yayin da suke gudanar da sallar Juma’a a ranar Juma’ar da ta gabata. Wannan bayani ya zo ne bayan Shugaban ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadai da sace ɗimbin masu ibadar, tare da…
Read More
EFCC ta saka tukwicin kashi biyar ga masu kwarmaton ɓoye dukiyar Nijeriya a ƙasashen waje

EFCC ta saka tukwicin kashi biyar ga masu kwarmaton ɓoye dukiyar Nijeriya a ƙasashen waje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Zagon ƙasa (EFCC), Mista Ola Olukoyede, ya yi alƙawarin bai wa masu fallasa bayanai a faɗin duniya lada tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 ga duk wanda ya bayar da sahihin bayani da zai taimaka wajen gano tare da kwato kuɗaɗe ko dukiyoyin Nijeriya da ake zargin ’yan Nijeriya masu rashawa sun wawashe suka kai ƙasashen waje. Olukoyede ya yi wannan kiran ne ranar Laraba yayin gabatar da jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na 43 kan laifukan tattalin arziki da aka…
Read More