28
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta ƙaryata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa matasan da ke zaune a yankin Nyanya sun sayar da ƙodarsu domin samun kuɗi, yayin da wani wakili a Mararaba ke sayen sassan jikin mutane. Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta bayyana a Abuja ranar Laraba cewa rundunar ba ta samu ko tabbatar da wani rahoto makamancin haka ba. Ta ce babu wata sanarwa ko saƙo da ya fito daga rundunar da ke tabbatar da…
