28
Aug
Daga ZAHARADDEEN ILIYASU a Kaduna Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group ta gudanar da gagarumin taron Maulidin Manzon Allah (SAW) na watan Rabi’ul-Awwal na shekarar 1448/2026 a Kaduna, inda aka shafe tsawon dare ana gudanar da ibadu da shirye-shirye daban-daban domin ƙarfafa soyayya ga Manzon Allah (SAW) da kuma koyarwarsa. Taron ya ƙunshi karatun Alƙur’ani, zikiri, rera yabo da salati ga Manzon Allah (SAW), gaisuwar sada zumunci, rabon kyaututtuka da takardun shaidar kammala haddace wasu littattafai, tare da gudanar da addu’o’i na musamman a ƙarshen taron. A yayin taron, babban Shehin Zawiyyar, Shehu Isma’ila Umar Almaddah, ya gabatar da dogon…
