Labarai

Liverpool ta ƙulla yarjejeniya da PSG kan Barcola

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Liverpool ta ƙulla yarjejeniyar baka da Paris Saint-Germain akan siyan ɗan wasa Bradley Barcola. A yanzu hada-hadar tana matakin ƙarshe bayan samun cimma matsaya a tattaunar ɓangarorin biyu, kamar yadda Fabrizio Romano ya ruwaito. An ƙulla yarjejeniyar ne akan Yuro miliyan 140, wato kwatankwacin Fam miliyan 120. Ainihin farashin shi ne £100m (€117m) da kuma €22m a matsayin ƙari. Tuni dai Barcola ya amince da koma Liverpool a yarjejeniyar kwantaragi mai tsawo Liverpool ta fara kwaɗayin siyo ɗan Faransan mai shekaru 23 ne ne tun watan Mayu. Da fari PSG tana neman Yuro…
Read More

Shugaban NFF, Ibrahim Gusau da manyan jami’an hukumar sun yi murabus yayin binciken biliyan N17

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) tare da wasu manyan jami'an hukumar sun ajiye muƙamansu bayan ƙorafe-ƙorafen al'umma da kuma binciken wasu biliyoyin kuɗaɗe da aka ware don harkar ƙwallon ƙafa. Jagorancin hukumar ya rushe ne bayan watanni yana fuskantar matsi kan rashin samar da kyawawan sakamako da nazarin kuɗaɗe. Al'amarin ya caɓe ne a lokacin da 'yan wasan Super Falcons suka gaza samun cancantar shiga gasar Kofin Duniya na Mata na 2027 da za a yi a Brazil, karo na farko da tawagar ta rasa damar tun bayan fara gasar a 1991…
Read More

Yadda maulidin a zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani ya ƙayatar a Kaduna

Daga ZAHRADDIN ILYASU Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group ta gudanar da gagarumin taron Maulidin Manzon Allah (SAW) na watan Rabi’ul-Awwal na shekarar 1448/2026, inda aka shafe tsawon dare har wayewar gari ana gudanar da al’amura daban-daban domin karfafa soyayya ga Manzon Allah (SAW) da ɗabbaƙa koyarwarsa a aikace. Taron ya ƙunshi karatun Al-Ƙur'ani, zikiri, rera yabo da salati ga Manzon Allah (SAW), da gaisuwar sada zumunci, da mika kyaututtuka da takardun shaidar kammala haddace wasu littattafai, baya ga addu’o’i na musamman da aka gudanar a karshen zaman. A yayin taron, babban shehin zawiyyar, Shehu Ismaila Umar Almaddah ya gabatar…
Read More

Mataimakin shugabar Tanzaniya ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Emmanuel Nchimbi, wanda shi ne mataimakin shugabar ƙasar Tanzaniya, ya yi murabus daga muƙaminsa yayin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a ƙasar gabashin Afirkan. Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da shari'ar hamɓararwa ta shugaban tsagin adawa, Tundu Lissu. A ranar Talata, Nchimbi ya miƙa takardar murabus, inda Shugaba Samia Suluhu Hassan ta karɓi matakin nasa, kamar yadda cibiyar yaɗa labaran fadar shugaban ƙasar ta bayyana. A cewar fadar, ajiye aikin nasa zai fara aiki ne a ranar 4 ga watan Satumba, wato wata goma cif kenan bayan kama aiki a…
Read More
Fiye da mutane biliyan ɗaya ne suke rayuwa a unguwannin awon igiya a duniya — Farfesa Abdulaziz Raji

Fiye da mutane biliyan ɗaya ne suke rayuwa a unguwannin awon igiya a duniya — Farfesa Abdulaziz Raji

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta fara wani taron ƙasa da ƙasa na tsawon kwanaki biyu, wanda Sashen Kimiyyar Ƙasa da Muhalli na jami’ar ya shirya, domin tattauna hanyoyin da za a ƙara sanya al’umma cikin ayyukan yaƙi da sauyin yanayi da kuma samar da birane masu ɗorewa da dacewa da rayuwa. Taron, wanda aka yi shi a sashin kimiyyar Ƙasa na jami'ar wanda shi ne karo na biyu, taken taron na bana shi ne: “Gina makoma mai juriya: Matsugunan da ba a tsara su ba da matakan yaƙi da sauyin yanayi da al’umma…
Read More
Jam’iyyar ADC ta ƙaddamar da jagororin yaƙin neman zaɓe a Kebbi

Jam’iyyar ADC ta ƙaddamar da jagororin yaƙin neman zaɓe a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirin ta na tinkarar babban zaɓen game-gari na shekarar 2027, ranar Laraba ɗin nan jam'iyyar ADC a jihar Kebbi ta ƙaddamar da jagororin yaƙin neman zaɓe. Da ya ke jawabi a wajen taron, ɗan takarar kujerar mataimakin gwamna Dakta Musa Zagi Argungu ya bayyana cewa, sanin kowa ne ya'yan jam'iyyar ADC mutane ne da suka san ya kamata, masu bin doka da oda da son zaman lafiya, saboda haka ne ta ke bin ƙa'idojin da dokokin ƙasa da na zaɓe suka gindaya saboda haka ana fatar za su cigaba da bin doka da…
Read More
DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan bindiga da dama sun halaka, an raunata sojoji biyu a harin Sifawa

DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan bindiga da dama sun halaka, an raunata sojoji biyu a harin Sifawa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rahotanni daga garin Sifawa a ƙaramar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto sun bayyana cewa yan bindiga da dama sun mutu yayin da sojoji biyu suka sami raunuka a wani artabu tsakanin sojoji da yan bindiga safiyar Laraba ɗin nan. Wani ganau ya labartawa wakilin Jaridar Blueprint Manhaja da cewa ana hasashen maharan sun taso ne daga maɓoyar su da ke jejin ƙauyen Horo a karamar hukumar Shagari da zummar mamayar wata ƙaramar barikin sojoji da ke garin Sifawa sai dai ko da suka kunno kai suka tarar sojojin suna cikin shirin ko ta kwana…
Read More
An gudanar da bikin hawan Gani a Daura

An gudanar da bikin hawan Gani a Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, na daga cikin ɗimbin jama'a da suka halarci hawan Gani da aka gudanar a Masarautar Daura. Wani gagarumin biki na gargajiya da ake gudanarwa duk shekara a matsayin wani ɓangare na bukukuwan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW). Hawan Gani na daga cikin muhimman al’adun Masarautar Daura, inda sarakuna, hakimai, dagatai, masu unguwanni da sauran al’umma ke fitowa cikin ƙayatattun kayan gargajiya domin nuna al’adun masarautar tare da yin murnar wannan rana mai albarka. Haka kuma makaɗa da mawaƙan gargajiya,wasan Kokawa da damben gargajiya na da…
Read More
Gwamna Sule ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas da sakatarori shida

Gwamna Sule ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas da sakatarori shida

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas a matsayin mambobin majalisar zartarwar jihar. Gwamnan ya kuma rantsar da sabbin sakatarori na dindindin kuda shida da sabbin masu bashi shawarwari na musamman guda 11 da wani mamba na hukumar kula da ayyukan shari’a ta jihar da kuma wani mamba na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar da akafi sani da NASIEC duk a yau Laraba 26 ga watan Augusta na shekarar 2026 da ake ciki a Lafiya babban birnin jihar. A taron rantsarwar gwamna Sule ya buƙaci su rungumi…
Read More
Gidauniyar Sultan ta yi niyyar yi wa yara 80,772 rigakafi a Zamfara

Gidauniyar Sultan ta yi niyyar yi wa yara 80,772 rigakafi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gidauniyar Sultan watau Sultan Foundation, ta ƙaddamar da wani babban shirin rigakafi a Jihar Zamfara da nufin yiwa yara 80,772 marasa allurar riga-kafi allura a ƙananan hukumomi bakwai waɗanda suka fi samun rashin yiwa yara rigakafi kafin Disamba 2027. An ƙaddamar da shirin, mai taken Z-TRACE: Bin diddigi a Zamfara da kuma daidaita allurar riga-kafi, a yau Laraba, a wani taron fara aiki na kwana ɗaya da aka gudanar a Karma Guest Inn, Gusau. Da yake gabatar da jawabin maraba, daraktan shirye-shirye na Gidauniyar Sultan Foundation, Aminu Inuwa Muhammad, ya ce Zamfara tana da kimanin…
Read More