26
Aug
Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Manyan baƙi da masu ruwa da tsaki a harkar raya harshen Hausa sun jaddada muhimmancin kare harshen da al’adun Hausawa, tare da kira ga al’umma, musamman matasa, da su rungumi harshen domin tabbatar da ɗorewarsa a wannan zamani na fasahar sadarwa. Sun bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Hausa ta duniya, wanda ya haɗa manyan baƙi daga ciki da wajen Jihar Kano, ciki har da sarakuna, malamai, masana da shugabannin al’umma masu ruwa da tsaki wajen bunƙasa harshen Hausa da kare al’adun Hausawa. Da yake gabatar da jawabinsa, Mai Martaba Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna,…
