Labarai

Ibrahim Masari hadimin Tinubú da gwamnan Yobe sun bai wa ƙungiyar Izala ta Sheikh Jingir tallafin N600m

Ibrahim Masari hadimin Tinubú da gwamnan Yobe sun bai wa ƙungiyar Izala ta Sheikh Jingir tallafin N600m

Daga UMAR GARBA a Katsina Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Masari da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, sun yi alƙawarin bayar da gudummawar Naira miliyan 600 domin gina Jami’ar Fortune da JIBWIS ke ginawa a Jihar Bauchi. Masari da Buni za su bayar da Naira miliyan 300 kowannensu. Sai dai gudummawar ta zo ne a lokacin da ake ta muhawara kan alaƙar siyasa da addini, musamman bayan Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya fito fili yana goyon bayan Shugaba Tinubu da sake zaɓensa a 2027. Jaridar Daily Trust ta…
Read More

2027: Abin da ya sa Tinubu ya jirkita jaddawalin yaƙin neman zaɓensa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An buƙaci Fadar Shugaban Ƙasa ta sake nazari akan haɗin mamban kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a 2027 ne saboda waɗansu dalilai da ka iya tozarta yaƙin neman zaɓen, kamar yadda rahotanni suka bayyana. An yi ta cece-kuce daga ciki da wajen jam'iyyar tun bayan fitar da jaddawalin a ranar Asabar, inda da dama suka riƙa ankararwa kan cire wasu sunaye da sanya wasu da ake da alamar tambaya akansu. A jaddawalin, an naɗa Shugaba Tinubu a matsayin shugaba da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin maitaimaki. Haka kuma, an naɗa Shugaban APC…
Read More

Gwamna Buni da mashawarcin Tinubu sun bada tallafin miliyan N600 don gina jami’ar JIBWIS

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Siyasa, Kabiru Ibrahim Masari, sun bayar da tallafin jimillar Naira miliyan 600 domin gina jami'ar Fortune University. Ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa'iƙamatus Sunnah (JIBWIS), reshen Jos ce ta samar da jami'ar a yankin Magama Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toron Jihar Bauchi, wadda ake aikinta tun a baya. Masari da Gwamna Buni sun sanar da tallafin ne a ranar Lahadi yayin wani taron wayar da kan al'umma kan shiga harkar siyasa na kwana ɗaya mai taken "Enhanced Political Participation…
Read More

Ƙungiyar AVRS ta yi jimamin rasuwar Jarumi Taiwo Hassan Ogogo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar kare 'yancin kafafen yaɗa labarai (AVRS), ta shiga sahun masana'antar finafinai wajen jimamin rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta, jarumi Taiwo Hassan da aka fi sani da Ogogo. A wata sanarwa da ta fitar ta hannun Shugaban kwamitin yaɗa labaranta, Sani Mu'azu a ranar Talata, AVRS ta ce jarumin ginshiƙi ne daga cikin ginshiƙan masana'antar finafinan Nijeriya kuma jarumin da ƙwarewarsa ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da harkar gaba a tsawon shekaru da dama. Ta bayyana cewa, bisa baiwar da yake da ita, ya kasance mai nishaɗantarwa da ilimantar da masu kallo,…
Read More

2027: Zan cire tallafin fetur, daga bisani na dawo da shi, inji Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar zai dawo da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a 2027, amma daga baya zai cire na wucin-gadi don daidaita lamuran tattali, inji Kakakinsa Paul Ibe. Ibe ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na AIT, inda ya ce shirin Atiku akan tallafi yana da bambanci da na gwamnatocin baya kuma zai fifita samar da ɗanyen mai da tacewa a cikin gida Nijeriya. A cewarsa, dawo da shi na wucin-gadi zai bai wa 'yan Nijeriya da kasuwanci damar numfasawa da farfaɗowa daga matsin tattali da ake…
Read More
2027: Ishaq Elayo zai ceto Nasarawa ta Kudu – Ibrahim Osabwa

2027: Ishaq Elayo zai ceto Nasarawa ta Kudu – Ibrahim Osabwa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hon. Ibrahim Osabwa darakta janar na ƙungiyar yaƙin neman zaɓe ta Injiniya Ishaq Dauda Elayo wato ɗan takarar kujerar sanata na Nasarawa ta Kudu ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress ADC yace ubangidan na sa shi ne ɗan takara da ya dace da zai bai wa mutanen yankin mazaɓar Kudancin jihar wakilci nagari mai ma’ana da magance matsalolin cigaba da ke fuskantar yankin. Osabwa ya bayyana haka ne a wata hira na musamman da ya yi da 'yan jarida a Keana. Yace Injiniya Elayo ya amsa kiran al’ummar yankin da suka daɗe suna kira gare…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta umarci sarakunan gargajiya su gabatar da ra’ayoyin jama’arsu kan kasafin kuɗin 2027

Gwamnatin Zamfara ta umarci sarakunan gargajiya su gabatar da ra’ayoyin jama’arsu kan kasafin kuɗin 2027

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ma'aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta Jihar Zamfara ta ƙaddamar da shirye-shirye don kimanta kasafin kuɗi na shekarar 2027 tare a taron masu ruwa da tsaki, inda ta yi kira ga majalisun masarautu da sarakunan gargajiya da su gabatar da ra'ayoyin al'ummar su a ranar Juma'a ko kafin Juma'a, 4 ga Satumba, 2026. Taron, wanda aka gudanar a ranar Talata a kwalejin fasaha da kimiyya (ZACAS) da ke Gusau, an yi masa taken "Shirye-shirye a yau, gina Zamfara mai albarka gobe." Da yake buɗe taron, kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Farfesa Yahaya Zakari, ya ce…
Read More
Ranar Hausa ta duniya: Kano za ta zama cibiyar bikin Hausawa a gobe

Ranar Hausa ta duniya: Kano za ta zama cibiyar bikin Hausawa a gobe

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Yayin da ake saura wasu sa'oi a gudanar da bikin ranar Hausa ta duniya ta shekarar 2026, an yi kira ga ɗaukacin al’ummar Hausawa da su fito domin nuna kishin harshensu, tarihinsu da al’adunsu. Za a gudanar da bikin ne a gobe Laraba, 26 ga Agusta 2026, a fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Najeriya, Amb. Alh. Sani Adamu Geza Garkuwan Hausawan duniya, a Kano. Shugaban majalisar masarauta ta Arewar mu duniyar mu African Chiefdom and Council, Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, shi ne ya yi kiran, inda ya bayyana bikin a matsayin wata muhimmiyar dama ta…
Read More

Adadin ‘yan ta’adda da ke tuba ya ƙaru da kaso 202 – Sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun haɗaka a Arewa maso Gabas, ƙarƙashin Atisayen HAƊIN KAI, sun samu ƙarin adadi mai yawa cikin ƙanƙanin lokaci na kwamandoji, mayaƙa da masu taimaka wa 'yan ta'adda da ke miƙa wuya ga rundunar sojoji. Rahotanni sun bayyana cewa, sama da 'yan ta'adda guda 150 ne suka miƙa wuya acikin wannan makon, wanda idan aka kwatanta da 50 da aka samu a makon da ya gabata, hakan na wakiltar ƙarin kashi 202. Kafin Mohammed Goni, jami'in yaɗa labarai na rundunar kuma na riƙo, shi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar…
Read More
ADC da CSO na Gwamnan Katsina suna hannun jami’an tsaro a Abuja

ADC da CSO na Gwamnan Katsina suna hannun jami’an tsaro a Abuja

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An tsare babban dogarin Gwamnan Katsina (ADC) da kuma babban jami’in tsaron gwamnan (CSO) a hedikwatar ’yan sanda da kuma ta hukumar DSS da ke Abuja kamar yadda jaridar “Katsina Times ta bayyana. Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an biyu suna hannun jami’an tsaro domin amsa tambayoyi. Rahotanni sun ce lamarin ya samo asali ne bayan lalata wasu manyan allunan tallace-tallacen siyasa da ke kan hanyar shatale-talen Modoji zuwa gidan Gwamnatin Katsina. Wasu daga cikin allunan na ɗauke da hotunan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da wasu manyan ’yan siyasa, ciki har da mai bai…
Read More