25
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta janye jaddawalin sunayen 'yan kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Felix Morka, ya bayyana rahotannin da ke yaɗa hakan a matsayin jita-jita, inda ya ce dukkan wani hukuncin da aka yanke kan kwamitin, za a ji shi ne daga bakin jam'iyyar a hukumance. Da yake magana da 'yan jaridar a safiyar yau Talata a Abuja, Morka ya ce APC ba ta janye jaddawalin ba kuma ra rahotannin da ake yaɗawa akan haka ba gaskiya…
