24
Aug
Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban asusun kula da Ilimi na gwamnatin jihar Nasarawa da ake kira NASETFund a turance Abubakar Adamu Idris ya samu digiri na uku a fannin jagoranci da ilimin harkokin ilimi daga jami’ar Atlantic International University. Wannan ya zo ne bayan ya samu nasarar kare rubutunsa na digiri ɗin ƙarƙashin kulawar manyan malamai da aka san su a faɗin duniya. A cikin wani bidiyo da aka fitar kwanan nan shugaban NASETFund din Abubakar Adamu Idris ya bayyana nasarar a matsayin sakamakon hakuri ta cikin ƙalubalen rayuwa da na karatu da kuma tsarin karatun digiri na…
