23
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja. Cibiyar kula da 'yancin zamantakewa da tabbatar da gaskiya da adalci a Nijeriya (SERAP), ta yi kira ga Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da ya yi amfani da ikon da dokar ƙasa ta bayar wajen bayyana ainihin adadin gudunmawar da ta halasta a bayar a harkokin siyasa ƙarƙashin Sashe na 91 na Dokar Zaɓe ta 2026. Haka kuma, SERAP ta roƙi hukumar da ta wallafa ainihin adadin da aka ƙayyade da kuma sanar da su ga jam'iyyun siyasa, 'yan takara, masu taimakawa da kuma al'ummar ƙasa domin tabbatar da biyayya…
