23
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa tsofaffin gwamnonin Kano, Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, sun rasa karfin siyasa a jihar. Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja, inda ya ce siyasar da aka gina bisa “cin amana” ba ta daɗewa. Ya ce rikicinsa da Ganduje ya fara ne lokacin da tsohon gwamnan ya fara ƙalubalantar tsarin siyasar da suka gina tare, yana mai cewa hakan ya janyo koma bayan siyasarsa.…
