11
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta buga mai nuni da 'yan Boko Haram da mayaƙan ISWAP sun kashe sojoji 20 a yankin Arewa maso-gabas. A sanarwar da rundunar ta fitar a Alhamis, Daraktan Sashen Hulɗa da Jama'a na rundunar, Brig.-Gen Mohammad Yerima, ya ce wannan labari ba shi da tushe balle makama. Ya ce an yaɗa labarin ne da manufar sanyaya wa al'umma guiwa game da sha'anin yaƙi da matsalolin tsaro da sojojin ke yi da ma su kansu sojojin da ke yaƙin. A cewarsa harin baya-bayan nan da aka kai wa…