14
Feb
Daga AISHA ASAS Masu satar mutane a jihar Neja sun kama mota (bas) sukutum mallakar gwamnatin Neja (NSTA) ɗauke da fasinjoji 21 a daidai ƙauyen Yakila a cikin ƙaramar hukumar Rafi. Bayanan da Manhaja ta samu, sun nuna motar ta fito ne daga garin Kontagora zuwa Minna, babban birnin jihar, inda ɓarayin suka tare ta a hanya. Sannan fasinjoji 21 da ke cikin motar, ɓarayin sun tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji, suna yi suna harbin bindiga a iska, lamarin da ya razana mazauna ƙauyen inda kowa ya yi gudun neman mafaka. Bayanai sun nuna yankin Yakila ya zama tamkar maɓuyar…