Labarai

Rikicin Biliri: Gwamanati ta kafa dokar hana zirga-zirga

Rikicin Biliri: Gwamanati ta kafa dokar hana zirga-zirga

Daga WAKILIN MU Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a garin Biliri da ke cikin ƙaramar hukmar Biliri, biyo bayan rikici da ya ɓarke a yankin. Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahin Abubakar Njodi, ya fitar a Juma’ar da ta gabata, ta nuna dokar ta soma aiki kai tsaye ba tare da wani jinkiri ba da zummar maido da lumana a yankin da rikicin ya shafa. “Gwamnatin jihar ta jaddada buƙatar zama da juna lafiya da kuma ƙoƙarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda haka gwamnati ta dakatar da haɗa kowane nau’i na…
Read More
Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalan Dikko

Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalan Dikko

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya miƙa taziyyarsa ga iyalai, dangi, abokan arziki, Gwamnatin Katsina da ma al’ummar jihar Katsina baki ɗaya dangane da rasuwar tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Fasa-kwauri, Abdullahi Dikko Inde. Babban Hadimin Shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ne ya bada sanarwar saƙon ta’aziyyar Buhari a Juma’ar da ta gabata. A cikin sanarwar, Buhari ya yaba da gudunmuwar da marigayin ya bai wa ƙasa a halin rayuwarsa, kana ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa. Haka nan, ya yi fatan Allah ya bai wa iyalan marigayin juriya da haƙurin wannan rashi.
Read More
Delta: Haɗarin mota ya ci jarirai 2 da wasu mutum 4

Delta: Haɗarin mota ya ci jarirai 2 da wasu mutum 4

Daga FATUHU MUSTAPHA Wani mummunan haɗari da ya auku a jihar Delta, ya ci ran jarirai biyu da na wasu mutum huɗu. Haɗarin ya auku ne a ranar Alhamis a kan babbar hanyar Asaba zuwa Ughelli cikin ƙaramar hukumar Oshimili ta Arewa. Bayanai sun nuna haɗarin ya auku ne a sakamakon aikin gyaran hanyar da ke gudana a yankin wanda hakan ya tilasta abubuwan hawa yin amfani da gefe ɗaya na hanyar. Sai dai wasu da abin ya faru a gabansu, sun ce gangacin direbobin da haɗarin ya rutsa da su na daga cikin dalilin da suka haifar da aukuwar…
Read More
Gumi ya shiga tsakani don neman kuɓutar da ɗaliban Kagara da aka sace

Gumi ya shiga tsakani don neman kuɓutar da ɗaliban Kagara da aka sace

Daga AISHA ASAS Alamu da dama kuma masu gamsarwa sun nuna fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Ahmed Gumi, ya shiga tsakani domin kuɓutar da ɗaliban nan su 27 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kagara, Jihar Neja, cikin wannan makon. Bayanai daga jihar Neja sun tabbatar da Sheikh Gumi ya ziyarci Neja ya samu ganawa da 'yan bindigar da suka kwashe ɗaliban a dajin Bangi a ranar Alhamis. Idan da dai za a iya tunawa, a daren Larabar da ta gabata 'yan bindigar suka kai hari a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a yankin ƙaramar…
Read More
Allah Ya yi wa Dikko rasuwa

Allah Ya yi wa Dikko rasuwa

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya, Abdullahi Dikko Inde, rasuwa a ranar Alhamis (18/02/2021). Iyalan marigayin ne suka bada bayanin tabbacin rasuwarsa. Sanarwar da ta fito daga hannun Mai Magana da Yawun Hukumar Kwastam na Ƙasa, DC Joseph Attah, ta nuna za a gudanar da jana'izar marigayin a ranar Juma'a (19/02/2021), bayan sallar Juma'a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja. A halin rayuwarsa, marigayin ya shugabanci Hukumar Kwastam daga 2009 zuwa 2015. Attah ya yi fatan Allah Ya bai wa iyalan marigayin danganar wannan rashi, tare da fatan Allah Ya sa Aljanna ta…
Read More
Neja: Bello ya tabbatar da sace ɗalibai 27 da wasu mutum 15 a yankin Kagara

Neja: Bello ya tabbatar da sace ɗalibai 27 da wasu mutum 15 a yankin Kagara

Daga BASHIR ISAH Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da 'yan bindiga sun sace ɗaliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara su 27 da ma'aikatar makarantar 3 da kuma wasu mutum 12, a garin Kagara cikin ƙaramar hukumar Rafi, jihar Neja. Bello ya tabbatar da faruwar haka ne ga manema labarai a ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala taron gaggawa da shugabannin tsaro a Minna, babban birnin jihar. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa 'yan bindigar sun shiga makarantar ne da misalin ƙarfe biyu na daren Laraba, inda suka kashe ɗalibi guda da sace…
Read More
Za mu yi maganin masu haifar da rikice-rikice a ƙasa, inji Buhari

Za mu yi maganin masu haifar da rikice-rikice a ƙasa, inji Buhari

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗora alhakin faruwar wasu rikice-rikice a sassan ƙasar nan kan attajirai da masu matsayi, tare da shan alwashin yin maganinsu. Buhari ya yi wannan magana ne a ranar Talata a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar dattawan Barno da Yobe a fadarsa da ke Abuja kamar dai yadda mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya bayyana. A sanarwar da Femi ya fitar Buhari ya ce, "Muna da buƙatar wannan ƙasa, za mu ci gaba da aiki domin samun daidaito. "Ina da yaƙinin cewa za mu shawo kan 'yan…
Read More
Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Daga WAKILIN MU Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana farin cikin sa kan yadda aka raba kuɗi naira miliyan tamanin ga matan jihar su 4,000 a ƙarƙashin shirin tallafa wa matan karkara da jari wanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa. Gwamnan ya faɗi haka ne lokacin da Ministar Harkokin Jinƙai Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta kai ziyara a jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya ce shirin na 'Cash Grant for Rural Women' zai taimaka wa matan jihar da dama wajen ficewa daga ƙangin fatara da yunwa. Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 21 a Neja

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 21 a Neja

Daga AISHA ASAS Masu satar mutane a jihar Neja sun kama mota (bas) sukutum mallakar gwamnatin Neja (NSTA) ɗauke da fasinjoji 21 a daidai ƙauyen Yakila a cikin ƙaramar hukumar Rafi. Bayanan da Manhaja ta samu, sun nuna motar ta fito ne daga garin Kontagora zuwa Minna, babban birnin jihar, inda ɓarayin suka tare ta a hanya. Sannan fasinjoji 21 da ke cikin motar, ɓarayin sun tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji, suna yi suna harbin bindiga a iska, lamarin da ya razana mazauna ƙauyen inda kowa ya yi gudun neman mafaka. Bayanai sun nuna yankin Yakila ya zama tamkar maɓuyar…
Read More
Masarautar Zazzau ta naɗa ɗanjarida a matsayin Ɗan Iiyya

Masarautar Zazzau ta naɗa ɗanjarida a matsayin Ɗan Iiyya

Daga WAKILIN MU Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya naɗa Alhaji AbdulRahaman Nuhu Bayero a matsayin sabon Ɗan Iyyan Zazzau. AbdulRahaman Nuhu Bayero ya maye gurbin marigayi Ɗan Iyan ne wanda ya rasu a Nuwamban 2020. Wasiƙar naɗin wadda ta sami sa hannun Sakataren Sarkin Zazzau kuma Sarkin Fulanin Zazzau, Alhaji Barau Musa Aliyu, ta nuna kwamitin naɗi zai sanar da ranar da bikin naɗin zai gudana. Masarautar ta taya AbdulRahaman Nuhu Bayero murnar samun wannan muƙami tare da addu'ar Allah ya taimaka masa. Sabon Ɗan Iyyan, ma'aikaci ne a sashen labaru da al'amuran yau a babban ofishin Radio…
Read More