Labarai

Allah Ya yi wa Dikko rasuwa

Allah Ya yi wa Dikko rasuwa

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya, Abdullahi Dikko Inde, rasuwa a ranar Alhamis (18/02/2021). Iyalan marigayin ne suka bada bayanin tabbacin rasuwarsa. Sanarwar da ta fito daga hannun Mai Magana da Yawun Hukumar Kwastam na Ƙasa, DC Joseph Attah, ta nuna za a gudanar da jana'izar marigayin a ranar Juma'a (19/02/2021), bayan sallar Juma'a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja. A halin rayuwarsa, marigayin ya shugabanci Hukumar Kwastam daga 2009 zuwa 2015. Attah ya yi fatan Allah Ya bai wa iyalan marigayin danganar wannan rashi, tare da fatan Allah Ya sa Aljanna ta…
Read More
Neja: Bello ya tabbatar da sace ɗalibai 27 da wasu mutum 15 a yankin Kagara

Neja: Bello ya tabbatar da sace ɗalibai 27 da wasu mutum 15 a yankin Kagara

Daga BASHIR ISAH Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da 'yan bindiga sun sace ɗaliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara su 27 da ma'aikatar makarantar 3 da kuma wasu mutum 12, a garin Kagara cikin ƙaramar hukumar Rafi, jihar Neja. Bello ya tabbatar da faruwar haka ne ga manema labarai a ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala taron gaggawa da shugabannin tsaro a Minna, babban birnin jihar. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa 'yan bindigar sun shiga makarantar ne da misalin ƙarfe biyu na daren Laraba, inda suka kashe ɗalibi guda da sace…
Read More
Za mu yi maganin masu haifar da rikice-rikice a ƙasa, inji Buhari

Za mu yi maganin masu haifar da rikice-rikice a ƙasa, inji Buhari

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗora alhakin faruwar wasu rikice-rikice a sassan ƙasar nan kan attajirai da masu matsayi, tare da shan alwashin yin maganinsu. Buhari ya yi wannan magana ne a ranar Talata a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar dattawan Barno da Yobe a fadarsa da ke Abuja kamar dai yadda mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya bayyana. A sanarwar da Femi ya fitar Buhari ya ce, "Muna da buƙatar wannan ƙasa, za mu ci gaba da aiki domin samun daidaito. "Ina da yaƙinin cewa za mu shawo kan 'yan…
Read More
Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Daga WAKILIN MU Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana farin cikin sa kan yadda aka raba kuɗi naira miliyan tamanin ga matan jihar su 4,000 a ƙarƙashin shirin tallafa wa matan karkara da jari wanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa. Gwamnan ya faɗi haka ne lokacin da Ministar Harkokin Jinƙai Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta kai ziyara a jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya ce shirin na 'Cash Grant for Rural Women' zai taimaka wa matan jihar da dama wajen ficewa daga ƙangin fatara da yunwa. Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 21 a Neja

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 21 a Neja

Daga AISHA ASAS Masu satar mutane a jihar Neja sun kama mota (bas) sukutum mallakar gwamnatin Neja (NSTA) ɗauke da fasinjoji 21 a daidai ƙauyen Yakila a cikin ƙaramar hukumar Rafi. Bayanan da Manhaja ta samu, sun nuna motar ta fito ne daga garin Kontagora zuwa Minna, babban birnin jihar, inda ɓarayin suka tare ta a hanya. Sannan fasinjoji 21 da ke cikin motar, ɓarayin sun tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji, suna yi suna harbin bindiga a iska, lamarin da ya razana mazauna ƙauyen inda kowa ya yi gudun neman mafaka. Bayanai sun nuna yankin Yakila ya zama tamkar maɓuyar…
Read More
Masarautar Zazzau ta naɗa ɗanjarida a matsayin Ɗan Iiyya

Masarautar Zazzau ta naɗa ɗanjarida a matsayin Ɗan Iiyya

Daga WAKILIN MU Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya naɗa Alhaji AbdulRahaman Nuhu Bayero a matsayin sabon Ɗan Iyyan Zazzau. AbdulRahaman Nuhu Bayero ya maye gurbin marigayi Ɗan Iyan ne wanda ya rasu a Nuwamban 2020. Wasiƙar naɗin wadda ta sami sa hannun Sakataren Sarkin Zazzau kuma Sarkin Fulanin Zazzau, Alhaji Barau Musa Aliyu, ta nuna kwamitin naɗi zai sanar da ranar da bikin naɗin zai gudana. Masarautar ta taya AbdulRahaman Nuhu Bayero murnar samun wannan muƙami tare da addu'ar Allah ya taimaka masa. Sabon Ɗan Iyyan, ma'aikaci ne a sashen labaru da al'amuran yau a babban ofishin Radio…
Read More
Abin da ya sa Fulani makiyaya ke riƙe bindiga, inji Gwamna Bala

Abin da ya sa Fulani makiyaya ke riƙe bindiga, inji Gwamna Bala

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, ya ce Fulani makiyaya kan riƙe bindiga ne saboda kare kai. Gwamnan ya faɗi a haka ne a lokacin da yake magana a wajen taron bikin Makon 'Yan Jarida wanda Reshen Wakilai na Ƙungiyar 'Yan Jarida a Jihar Bauchi ya shirya. Ya riƙe bindiga kan taimaka wajen hana ɓarayi su kai musu hari su kashe su sannan su yi gaba da shanunsu. Yana mai cewa gazawar gwamnati wajen bai wa makiyayan kariya shi ya ya sa su kuma suka ɗauki matakin kare kansu daga ta'addancin 'yan ta'adda. "Saboda shi Bafulatani mutum…
Read More
Oyo: An gano manomi a mace a gonarsa

Oyo: An gano manomi a mace a gonarsa

Daga AISHA ASAS An gano wani manomi mai suna Bashiru Akinlota mace a gonarsa da ke Itigbo a hanyar Apodun, Igangan a cikin ƙaramar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar Oyo. Binciken Manhaja ya gano cewa wannan al'amari ya auku ne a Larabar da ta gabata bayan da marigayin ya fahimci gonarsa ta koko da kashu ta kama da wuta inda ya je don kashe wutar. Bayanai sun nuna marigayin ɗan shekara 65, ya yanke jiki ne ya faɗi a daidai lokacin da ya yi ƙoƙarin kashe wutar da ta kama gonarsa. Kwamandan Rundunar Tsaro ta Amotekun a Oyo, Col…
Read More
Galibin makiyayan da ke halaka mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji Ortom

Galibin makiyayan da ke halaka mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji Ortom

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa galibin makiyayan da ke halaka mutane a ƙasar nan ba 'yan asalin Nijeriya ba ne. Bayanin haka ya fito ne ta bakin Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata. Ortom ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya buƙaci a sake waiwayar dokokin ECOWAS don yin gyarar fuska dangane da sha'anin zirga-zirgar mutane da kayayyaki a nahiyar Afirka. Ya ce makiyaya daga wajen Nijeriya na amfani da damar zirga-zirga wajen ruruta matsalolin tsaro. Ta bakinsa, "Ƙasashe maƙwabta irin…
Read More
Runduna ta ƙaryata labarin kashe sosjoji 20

Runduna ta ƙaryata labarin kashe sosjoji 20

Daga FATUHU MUSTAPHA Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta buga mai nuni da 'yan Boko Haram da mayaƙan ISWAP sun kashe sojoji 20 a yankin Arewa maso-gabas. A sanarwar da rundunar ta fitar a Alhamis, Daraktan Sashen Hulɗa da Jama'a na rundunar, Brig.-Gen Mohammad Yerima, ya ce wannan labari ba shi da tushe balle makama. Ya ce an yaɗa labarin ne da manufar sanyaya wa al'umma guiwa game da sha'anin yaƙi da matsalolin tsaro da sojojin ke yi da ma su kansu sojojin da ke yaƙin. A cewarsa harin baya-bayan nan da aka kai wa…
Read More