Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalan Dikko

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya miƙa taziyyarsa ga iyalai, dangi, abokan arziki, Gwamnatin Katsina da ma al’ummar jihar Katsina baki ɗaya dangane da rasuwar tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Fasa-kwauri, Abdullahi Dikko Inde.

Babban Hadimin Shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ne ya bada sanarwar saƙon ta’aziyyar Buhari a Juma’ar da ta gabata.

A cikin sanarwar, Buhari ya yaba da gudunmuwar da marigayin ya bai wa ƙasa a halin rayuwarsa, kana ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa.

Haka nan, ya yi fatan Allah ya bai wa iyalan marigayin juriya da haƙurin wannan rashi.