19
Mar
Matawalle Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da ba su tuba ba sun afkawa ƙauyen Kabasa da ke Gundumar Magami a Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara, sun kashe mazauna ƙauyuka biyar da kuma sojoji uku da suka haɗa da Manjo wanda Kwamanda ne dake wakiltar Yankunan Magami, Dankurmi da Dansadau tare da ƙone motar sojojin. Wani mazaunin yankin mai suna Malam Lawali Magami a wata hira ta wayar tarho tare da Manhaja a Gusau ya ce, ’yan ta'addan sun yi wa ƙauyen qawanya da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Talata, suka fara…