Buhari ya jinjina wa Uzodinma kan ayyukan cigaba

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da ya ɗore da ayyukan cigaba da gwamnatinsa ke yi don kyautata rayuwar talakawan jiharsa.

Talatar da ta gabata Shugaba Buhari ya yi wannan kira, tare da yaba ƙoƙarin Gwamna Uzodinma na kammala tarin ayyukan cigaba a tsakanin shekara guda.

Buhari ya yi kalamansa ne ta bidiyo yayin ƙaddamar da wasu hanyoyi guda biyu a garin Owerri, babban birnin jihar waɗanda aka kammala aikinsu cikin shekara guda da gwamnan ya yi kan mulki.

Buhari ya jinjina wa gwaman dangane da kammala hanyar Assumpta Cathedral zuwa mararrabar babbar asibiti, da kuma hanyar Bankin Duniya zuwa Sakatariyar Gwamnatin Tarayya.

A cewar Buhari, hanyar Assumpta ita ce mahaɗar shiyyar Kudu maso-gabas da Kudu maso-kudu. Yayin da hanyar da ta taso daga wajen Bankin Duniya, hanya ce mai muhimmanci da take sadar da jama’a da sakatariyar tarayya.

Shugaban ya ce ya yi matuƙar murna da aikin waɗannan hanyoyi ya zama daga cikin ayyukan da gwamnan ya ƙaddamar daidai lokacin da ya cika shekara guda da kama mulkin jiharsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *