Yadda ’yan bindiga suka kashe Sojoji 4 da ƙona motar su a Zamfara

Matawalle

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da ba su tuba ba sun afkawa ƙauyen Kabasa da ke Gundumar Magami a Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara, sun kashe mazauna ƙauyuka biyar da kuma sojoji uku da suka haɗa da Manjo wanda Kwamanda ne dake wakiltar Yankunan Magami, Dankurmi da Dansadau tare da ƙone motar sojojin.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Lawali Magami a wata hira ta wayar tarho tare da Manhaja a Gusau ya ce, ’yan ta’addan sun yi wa ƙauyen qawanya da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Talata, suka fara harbin kan mai uwa da wabi a kan al’ummar, inda ya ƙara da cewa an kashe mazauna ƙauyuka biyar nan take.

Ya ci gaba da cewa, a lokacin da suka ga sojoji na haɗin gwiwar atisayen Sahel Sanity Operation don daƙile harin, ’yan ta’addan sun yi aman wuta ga sojojin, inda suka kashe Manjo tare da jami’an sa biyu, sannan suka ƙona motar aikin yayin musayar wutar.

Ya ƙara da cewa tuni gawarwaki takwas ciki har da sojojin da suka mutu aka tafi da su Gusau kuma yanzu haka suna Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, inda ya qara da cewa, mazauna ƙauyukan da dama sun ji rauni yayin da suke qoqarin tserewa daga harin ’yan ta’addan.

“Kamar yadda nake magana da kai, a halin yanzu gawarwakin mutanen ƙauyukan da aka kashe da sojoji 3 da aka kashe an tafi da su Gusau kuma ba zan iya tantance ainihin adadin waɗanda suka samu rauni a yayin harin da aka kai ƙauyen namu ba, amma dui abin da na sani cewa mutane da yawa sun ji rauni,” inji Lawali Mustafa Magami.

Rahoton na Manhaja ya nuna cewa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bada wa’adin watanni biyu ga ’yan ta’addan da suka addabi yankin arewacin ƙasar bakiɗaya, da su ajiye makaman su ko kuma su fuskanci matakan soji.

A kuma yayin da Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ta fara aiki kan shirin sasantawa da zaman lafiya tare da ’yan bindigar, inda ɗaruruwan ’yan bindiga suka miƙa makaman su suka rungumi zaman lafiya tun lokacin da aka ɓullo da shirin sulhun zaman lafiyar a farkon shekarar da ta gabata a jihar.

Duk da haka, ƙoƙarin jin ta bakin rundunar a ƙarƙashin sashin watsa labarai na rundunar sojin ta Sahel Sanity kan lamarin da wakilin mu ya yi ya ci tura har zuwa lokacin haɗa rahoton, amma wata majiya mai tushe da aka rufe ga sojojin da ke aikin atisayen Sahel na jiha a jihar ta Zamfara da ba a bayyana sunanta ba, ta tabbatar da harin da aka kai wa jami’an su wanda ya kai ga kashe uku daga cikin jaruman sojoji waxanda suka haɗa da guda da ƙananan sojoji biyu.

A wata mai kama da haka, Gwamnatin Jihar Zamfara qarqashin jagorancin Mai Girma Gwamna Bello Muhammed Matawalle ta nuna damuwar ta kan harin da wasu ’yan bindiga masu tayar da qayar baya suka kai kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙauyen Kabasa da ke gundumar Magami a Ƙaramar Hukumar Gusau ta jihar, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ibrahim Magaji Dosara ya faɗa a cikin wata sanarwa.

A cewar sa, Gwamna Matawalle ya yi baqin ciki da damuwa game da wannan abin takaici, kuma ya yi Allah-wadai da shi wanda ya haifar da asarar rayuka a ƙauyen Kabasa tare da miqa ta’aziyar sa ga iyalan waxanda aka kashe.

“Tuni gwamnati ta umarci hukumomin tsaro a jihar da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin sannan su kawo rahoto ga gwamnati don ɗaukar mataki yayin da aka umarci kwamiti na dindindin don tantance asarar da aka yi wa al’umma,” a cewar kwamishina.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jama’ar da abin ya shafa tare da shawartar su da su kasance masu bin doka da oda da gudanar da harkokin su na yau da kullum.