‘Yan bindiga sun yi niyyar halaka ni ne – Sarkin Birnin Gwari

Alh. Zubairu Jibril

Daga MUHAMMAD AHMAD a Kaduna

A sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai wa tawagar  Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, sarkin ya ce an yi niyyar halaka shi ne, amma sai aka samu kuskure ba ya cikin motar tasa.

Sarkin ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan harin da aka kai wa tawagar tasa a jiya Alhamis, a kan hanyar su ta zuwa Kaduna domin yin taro da gwamnan jihar, yana mai cewa akwai haɗin bakin wasu daga cikin al’ummar Birnin Gwari.

Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ce “Akwai kyakkyawan zato cewa ’yan bindigar ba za su yi wannan abu ba sai da taimakon wasu. Ka ga idan ka dubi mota ta, ai ka ga sun yi niyya ne su yi kisan kai, domin ka dubi gilas ɗin gaba yadda suka tarwatsa shi. Sannan kuma daidai wurin da na ke zama an fasa gilas ɗin da harsashin bindiga”

“Ka ga kenan hakan na nufin sun yi niyyar su kashe mu ne. Irin wannan kuma ba ka fid da zaton cewa akwai waxanda suke tare da mu da ke ba su irin wannan sanarwar,” a cewar sa.
Sarkin ya ƙara da cewa “An yi sa’a ba samu asarar rai ba, kawai fargaba ce irin ta ɗan adam wadda dole sai da suka sha magani daga baya suka samu waraka.

Sarkin ya ce wasu suna ganin ma’adinan zinaren da ke ƙarƙashin ƙasa a yankin ne suka sanya ake tsananta kai hare-hare a yankin nasu.

“Da yawa na cewa ma’adanin gwal da muke da shi ne ya ja muka samu kanmu cikin wannan rikici, to me ya sa ba za a je a nemi gwal xin ba a rabu da mu, sai a yi ta kashe mu ana hana mu ci gaba,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *