Kwara: Fahimtar juna game da hijabi

Daga IBRAHIM SHEME

Sau da yawa, na kan yi mamakin yadda wasu ’yan Nijeriya ba su so a zauna lafiya; kullum ƙoƙari su ke yi su tsokano wata magana da za a dinga tada jijiyar wuya a kan ta. Dubi dai tataɓurzar da ake yi kan batun saka hijabi na ’yan makaranta mata Musulmi a Jihar Kwara. Wasu Kiristoci sun tashi haiqan a kan cewa ba su yarda mata ɗalibai su sanya hijabi su je makaranta ba.

Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne masu wannan kamfen ɗin ba wai wasu zauna-gari-banza kaxai ba ne, waɗanda za a ce ƙila ba su da masaniya kan gaskiyar lamarin; a’a, mutane ne masu ilimi, shugabannin al’umma irin su shugaban ƙungiyar addinin Kirista mabiya ɗariƙar Baptist ta Jihar Kwara, Victor Dada, wanda ya na daga cikin masu tada jijiyar wuya a kan wannan al’amari. Har ta kai sun fito sun yi zanga-zanga a Ilorin, su na faɗin ba su yarda ba.

Babbar matsayar Kiristoci ita ce makarantun da ake magana a kan su na Kirista ne, wato makarantun mishan, irin waɗanda ƙungiyoyin addini su ka kafa tun kafin samun mulkin kai zuwa bayan samun mulkin kai. A cewar su, waɗannan makarantu an kafa su ne a bisa ruhi da aƙidar Kiristanci, kuma akwai ƙa’idoji na yadda ɗalibai za su riƙa yin shiga ko gudanar da rayuwar su a cikin su.

Idan mun dubi wannan matsaya tasu, za mu ga cewa akwai jirwayen da aka yi wa gaskiya a cikin ta. Wato an nuno wani abu mai kama da gaskiya, amma kuma a cikin sa akwai ƙarya. A kan wannan na ke so mu samu fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista.

Na farko dai, ba Kwara ce farau ba kan wannan magana ta sanya hijabin ɗalibai a makarantun sakandare. An yi irin muhawarar a jihohi da dama, daga baya aka samu fahimta, aka wuce wurin. Jihohin sun haɗa da Legas, Osun, Oyo, Ekiti  da Kaduna. Yanzu a waɗannan jihohi, ɗalibai mata kan sanya hijabi a kan yunifom ɗin su, kuma babu wanda ya cutu. Su ma akwai lokacin da muhawarar ta taso kamar baƙin hadari.

Mu yi nazarin matsayar Kiristocin Kwara wadda na ce ƙarya ce mai jirwayen sofanen gaskiya. Na farko dai, gaskiya ne an kafa makarantun mishan ne a kan aƙidar addini, kuma akwai ƙa’idojin yin mu’amala a cikin su. To amma kuma ƙarya ce da ake cewa wai makarantun na mishan ne a yau. Dalili shi ne tun a cikin 1974 gwamnatoci ta karve dukkan makarantun mishan, ta maida su na gwamnati a duk faɗin ƙasar nan. Ta yi haka ne domin a zauna lafiya kuma a kauce wa ilimantar da yara manyan gobe a kan tafarkin addini kaɗai.

Wannan hangen nesan da aka yi, ba makarantun Kirista kaxai aka karɓe ba, har da na Musulmi irin su Kwalejin Sardauna da ke Kaduna. Tun daga ranar da su ka koma hannun gwamnati, gwamnati ce ke gudanar da su; ita ke ɗaukar ɗalibai, ita ke ɗaukar ma’aikata da biyan su albashi, ita ke gina ajujuwa, ofisoshi da ɗakunan kwana, ita ke shirya jarabawa, ita ke komai. Daga lokacin, babu wata ƙungiyar addini (ta Kirista ko ta Musulmi) da aka qara bari ta gudanar da makaranta.

Da gaske ne, bayan shekaru wasu qungiyoyin addini sun je kotu a kan ba su yarda da ƙwace masu makarantu da aka yi ba. An tafka shari’a a Babbar Kotu, aka ba gwamnati gaskiya; su ka ɗaukaka qara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, a nan ma aka ba gwamnati gaskiya. To ina kuma gaskiyar su ta ke? Wasu ƙungiyoyin sun ƙara ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli, amma yanzu an yi shekaru ba a yi komai game da qarar ba. Tunda kuwa haka ne, makarantun na waye? Na gwamnati ne. A Kwara ma, gwamnatin jiha ta kafa doka mai suna ‘Kwara State Education Law of 1996 (CAP E1)’ wadda ta jaddada wa gwamnati hurumin mallakar waɗannan makarantu.

Bayan haka, Sashe na 38 na Tsarin Mulkin Nijeriya ya bada dama ga mata Musulmi su sanya hijabi a wurin aiki ko a makaranta. Don haka matsayar gwamnati ita ce an ba kowane ɗalibi damar ya yi shigar da ta dace da addini sa da al’adar sa. Wannan ne ya sa za ka ga ’ya’yan Musulmi mata sun ɗora hijabi a kan yunifom xin su, kuma sun sanya dogon wando, su kuma ’ya’yan Kirista mata sun sanya siket da riga. Ko su Musulman, ba a ce tilas sai yarinya ta sanya hijabin ba, idan ba ta so ko kuma iyayen ta ba su so, shi kenan.

Su kan su Kiristoci fa addinin su ya ki kira ga matan su da su rufe jikin su domin jikin mace al’aura ne. Mu dubi hotunan mata Kiristoci na zamanin da, mu ga yadda su ke rufe jikin su ruf da tufafi. Har ma akwai matan addinin ko ɗalibai, wato ‘nuns’, waɗanda za ka ga sun yi shiga ta mutunci har da xora hijabi. Duk da haka, ba wanda ya tilasta wa matan Kirista yin shiga irin ta waxanda su ka gabace su. Yanzu Turanci ya yi wa kowa yawa, ga shi an gurvata addini da al’adu, wanda hakan ya sa wasun su na ganin kamar yin sanya siket da guntuwar riga wayewa ce ko kuma wani nau’i na bautar su. Saboda haka ba za mu ce tilas su sanya hijabi ba, wanda tuni su ka ce shi alama ce ta Musulunci.

To amma abin da na lura da shi shi ne masu adawa da sanya hijabi ba su da ilimin addini, sannan akwai waxanda munafinci da gabar addini ke damu. Idan ba domin haka ba, to da sun san cewa addinin su ya buqace su da su suturta jikin su. To amma saboda sun zama baƙaƙen Turawa, ba za su gane ba. Shin Musulmi sun tilasta su sanya hijabi ne? Abin da Musulmi ke cewa shi ne, “Mu za mu sanya hijabi domin addinin mu ya ce mu sanya, ku kuma ku sanya abin da ku ka dama”, amma su kamar cewa su ke, “Ba za mu qyale ku ku sanya abin da ku ke so ku sanya ba, amma mu za mu sanya abin da mu ke so mu sanya!” Irin wannan tsokana har ina?

Ya kamata Kirista su gane cewa sanya hijabi a wajen Musulmi umarni ne na Allah (s.w.t.). Ba ‘fashion’ ba ne. A cikin Alqur’ani (Sura ta 24:31) Allah ya umarci mata muminai da su sanya hijabi, kuma akwai hadisai inda Manzon Allah (s.a.w.) ya ce a bi wannan umarnin. Tunda kuwa haka ne, yaya wani wanda ba Musulmi ba zai hana Musulmi yin addinin sa bayan kuwa shi bai hana Kirista yin nasa addinin ba?

Ya kamata masu kaɗa gangar zuga a Kwara su daina. Ai ba su fi Kiristocin Kaduna ko Ekiti son addini ba, amma su waxancan sun gane cewa saka hijabi wani haƙƙi ne na Musulmi wanda ba ya ƙwatuwa domin kundin Tsarin Mulki ya amince masu. Kai, ko a Amurka an ƙyale mata Musulmi su sanya hijabi a wurin aikin gwamnati.

An fahimci matsayin sa a Musulunci, sannan uwa-uba ba a ga inda ya cutar da wani ba. Ya kamata jama’ar Kwara su zauna lafiya da junan su. Su sani cewa tada hankali a kan wannan batu shirme ne, domin kuwa ba shi ne abin da ya damu talakan Nijeriya ba. Mu abin da ya dame mu shi ne fatara, rashin tsaro, rashin aikin yi da shaye-shaye. Su kaxai sun ishe mu daga, ba sai an kunno mana wata wutar ba.