Nijeriya ta shiga sahun ƙasashe mafiya haɗarin rayuwa – Ƙungiyar GTI

Daga UMAR M. GOMBE

Sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaron da suka mamaye wasu sassan Nijeriya, Ƙungiyar dake sanya ido kan ayyukan ta’addanci ta duniya wato “Global Terrorism Index” (GTI), ta bayyana ƙasar nan a matsayin ɗaya daga cikin mafi haɗari wajen rayuwa a faɗin duniya.

Rahoton ƙungiyor na shekarar 2020 da aka gabatar, ya nuna cewa an samu ƙaruwar hare-haren mayaƙan Boko Haram da kashi 25 cikin ɗari, yayin da kashe-kashen da ’yan bindiga ke yi kuma ya ƙaru da kashi 26 cikin ɗari, savanin waɗanda aka gani a shekarar 2019.

“Ƙasashen da ke gaban Nijeriya wajen fuskantar irin waɗannan matsaloli a duniya kawai su ne Ƙasashen Iraƙi da Afghanistan waɗanda matsalolin tsaron suka yi ƙamari cikin su.”

“A tsakanin watan Fabrairun shekarar 2020 zuwa watan Fabrairun bana, an kashe mutane 2,769 a Jihar Barno kawai, yayin da garkuwa da mutane domin karvar kuɗin fansa ya ƙaru tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga a cikin shekaru 5 da suka gabata,” inji ƙungiyar.
Ƙungiyar ta kuma ƙara da cewa, tsakanin bara zuwa bana an biya kuɗin da ya kai dala miliyan 18 a matsayin diyyar mutanen da aka yi garkuwa da su.

Global Index ta ce yayin da matsalar tsaro ya zama jiki a Nijeriya, arewacin ƙasar nan ya fi fuskantar raɗaɗin wannan matsala, sakamakon hare-haren Boko Haram da harin ’yan bindiga da rikici tsakanin makiyaya da manoma da masu garkuwa da mutane da kuma rikice- rikicen dake da nasara da ƙabilanci da addini.

Rahotan ƙungiyar ya ƙara da cewa, ƙananan yara ma ba su tsira ba wajen fuskantar waɗannan matsaloli, ganin yadda a yankin Arewa maso gabas a ke kashe su da sace su da cin zarafin su da kuma amfani da su a matsayin sojojin haya, duk da matsalolin da suke fuskanta na rashin muhalli da kuma rashin abinci mai gina jiki.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla yara 4,000 aka kashe tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016 a Nijeriya, yayin da Hukumar UNICEF ta ce daga cikin mutane kusan miliyan 2 ne suka rasa muhallin su, inda kashi 60 daga ciki yara ne ƙanana.