Hare-haren Boko haram ya raba mutane sama da miliyan biyu da muhallin su – Rahoto

Daga MUAHAMMAD AL-AMEEN

A wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, ya bayyana cewa hare-haren mayaƙan Boko Haram sun raba mutane sama da miliyan biyu da muhallin su a Arewa-maso-Gabas, ya kuma haifar da lalacewar kayan more rayuwa da wahalar samun kula da lafiya ga mutanen da suka tsere daga gidajen su.

Rahotan ya ƙara da cewa ƙungiyoyin jinƙai da yawa sun damu da halin da mutanen yankin ke ciki, inda waɗan su suka yi ƙoƙarin janyo hankali kan tavarɓarewar al’amura ganin yadda annobar korona ta ɗauke hankalin duniya a halin da ake ciki.

Masu aikin jinƙai sun bayyana baƙin cikin su kan koma-bayan da ake samu na kuɗaɗen agaji daga masu taimakawa domin kula da mazauna yankin Arewa maso Gabas, ganin yadda matsalar tsaron yankin ya kwashe sama da shekaru 10 ana fama da shi.

Yanzu haka a yankin mutanen da aka raba da muhallin nasu na ƙoƙarin sake gina rayuwar su, kuma waɗannan mutane na ci gaba da fama da matsalar tsaro inji rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *