Ƙarin kuɗin wutar lantarki dakushe tattalin arzikin ƙasa ne – Atiku

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na babbar jam’iyyar hamayya, PDPD, Alhaji Atiku Abubakar, ya shiga sahun ‘yan Nijeriya da ke ci gaba da sukar matakin ƙarin kuɗin wutar lantarki da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka.

Atiku ya ce, ya yi amannar wannar ƙarin kuɗin wutar babu abin da zai tsinana in ba da ƙara dakusar da tattalin arzikin ƙasar nan tare da ƙara tsananta wa ‘yan ƙasa tsadar rayuwa.

Kwanan nan aka ji Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta sanar da ƙarin wuta amma a kan masu amfani da lantarkin na rukunin farko, ‘Band A’, a matsayin yunƙuri na dakatar da biyan tallafin lantarki.

Rukunin Band A, su me masu samun wutar lantarki na sa’o’i aƙalla 24 duk yini.

Sai dai, Atiku ya ce gwamnati ba ta yi farar dabara ba da wannan mataki da ta ɗauka saboda hakan zai ƙara daburta wa ƙasa lamarin tattalin arzikinta wanda kawo yanzu take fama da hauhawar farashin kayayyakin masarufi wanda ya kai kashi 31.70.

Jigon siyasar ya bayyana a shafinsa na X a ranar Juma’a cewa, “Ƙarin kuɗin wutar lantarki a daidai wannan lokaci da ‘yan Nijeriya ke fama da tsadar rayuwa sakamakon janye tallafin fetur.

“Gwamnati ta samu nasarar cire wa ‘yan ƙasa raɗaɗin janye tallafin mai ba sai ga shi ta kara musu wani. Ƙarin kuɗin lantarki zai zai ƙara jefa ‘yan ƙasa cikin mawuyacin hali….,” in ji Atiku.