‘A Legas Tinubu zai yi Ƙaramar Sallah’ – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

A wannan Lahadin ake sa ran Shuganq Ƙasa Bola Tinubu zai bar birnin tarayya Abuja zuwa Legas gabanin bikin Ƙaramar Sallah na bana.

Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken ‘Shugaba Tinubu zai Idil Fiɗr a Legas’ wadda ya fitar a ranar Asabar.

A cewar Ngelale, “Yayin bikin wanda ke nuni da ƙarewar watan Ramadan, Shugaban zai yi wa Nijeriya addu’o’i tare da ahalinsa.”

Sai dai sanarwar ba ta fayyace ranar Tinubun zai koma Abuja ba, amma cewa Shugaban zai ci gaba da gudanar harkokinsa lokacin hutun bikin sallar da bayan haka.