15
Oct
Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Muƙaddashin Kwanturola na gidan gyara jalin da ke Bauchi, Musa Dauda Doguwa ya buƙaci gwamnatocin lardin arewacin ƙasar nan da su kafa ma’aikatu na koya wa matasa sana’o’i da zummar rage gararambar su. Doguwa ya bayyana cewar, ya yi ayyuka a gidajen gyara hali daban-daban da ke sassan ƙasar nan, waɗanda suka haɗa da na Kano, Jigawa, Neja, Kaduna, Katsina, da sauransu. Amma bai taɓa iske gidan maza da yake da tarin matasa kamar na Bauchi ba. Doguwa ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan da kwamitin da ke…
