Kasuwanci

Kuɗin intanet: Majalisa ta gayyaci shugaban CBN don ya yi ƙarin haske

Kuɗin intanet: Majalisa ta gayyaci shugaban CBN don ya yi ƙarin haske

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa domin kare batun haramta hada-hadar kuɗaɗen intanet (crypto currencies) da gwamnati ta yi. Majalisar ta gayyaci Emefiele ne domin ya yi mata ƙarin haske kan irin damarmaki da kuma haɗarin da ke tattare da harkar kuɗaɗen intanet ga tattalin arzikin ƙasa. A can baya, Babban Bankin, ta hannun Daraktan Sashen Sanya wa Bankuna Ido Bello Hassan, ya bayyana cewa waɗannan kuɗaɗe na intanet wasu da ba a san ko su wane ne ba suke bada su kuma ba tare da wasu sanannun dokoki ba.…
Read More
Makinde ya sake buɗe kasuwar Shasha

Makinde ya sake buɗe kasuwar Shasha

Daga AISHA ASAS Bayan shafe kimanin makonni biyu da rufe kasuwar Shasha a jihar Oyo sakamakon ɓarkewar rikici a tsakanin 'yan kasuwan kasuwar, Gwamna Seyi Makinde ya bada umarnin sake buɗe kasuwar ba tare da wani jinkiri ba. Makinde ya buƙaci sake buɗe kasuwar ne yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin Hausawa da Yarabawan yankin a fadar gwamnatin jihar da ke Ibadan. Gwamnan ya ce an ɗauki matakin sake buɗe kasuwar ne duba da yadda rufe kasuwar ya yi tasiri kan tattalin arzikin yankin da ma jihar baki ɗaya. Ya ce yayin da ya ziyarci Sarkin Sasa da…
Read More
Ganduje ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa abinci a kano

Ganduje ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa abinci a kano

A Juma'ar da ta gabata Gwamnan Jihar Kano, Umar Ganduje, ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa abinci na Mamuda Foods, a yankin rukunan masana'antu da ke Challawa. Babban Ministan Kasuwanci da Masana'antu, Hon Niyi Adebayo, da Ƙaramar Minitar Kasuwanci, Hajiya Maryam Yalwaji Katagum, su ne suka mara wa gwamnan baya wajen ƙaddamar da kamfanin.
Read More
NAFDAC ta garƙame masana’antu 13 a Kano

NAFDAC ta garƙame masana’antu 13 a Kano

Daga AISHA ASAS Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta ce ta garƙame wasu masana'antun sarrafa madara a jihar Kano saboda rashin yin rijista da hukumar. Kodinetan NAFDAC a Kano, Alhaji Shaba Mohammad ne ya shaida wa manema labarai haka jim kaɗan bayan kammala aikin rufe masana'antun a ranar Alhamis. Jami'in ya ce hukumar ta dukufa aiki wajen ganin ta bankaɗo masu yin jabun kayayyaki suna saida wa jama'a domin kare lafiyar al'umma. Ya ci gaba da cewa, bayan sun bincika sun gano waɗannan wurare na sarrafa abubuwa mara inganci sai suka sunkuya aiki inda suka…
Read More
Kwastam ta kama kayayyakin da harajinsu ya haura milyan N74 a shiyyar Kaduna

Kwastam ta kama kayayyakin da harajinsu ya haura milyan N74 a shiyyar Kaduna

Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a shiyyar 'Zone B' mai hedikwata a Kaduna ƙarƙashin jagorancin Comptroller AB Hamisu, ta samu nasarar kama kayyakin da aka yi fasa-ƙwaurinsu wanda harajinsu ya haura Naira miliyan 74. Bayanan hukumar sun nuna wannan kamen da hukumar ta yi ya faru ne cikin Fabrairun da ake ciki, ciki har da gano ɗaruruwan buhun shinkafar ƙetare da aka ɓoye a rumbunan ajiya daban-daban sassan shiyyar. A cikin takardar sanarwa ga manema labarai da ta fito ta hannun Mai Magana da yawun hukumar na shiyyar Zone B, ASC1 MA Magaji, Hamisu ya lissafo…
Read More
Rikicin Kasuwa: Gwamnonin sun ziyarci Shasha

Rikicin Kasuwa: Gwamnonin sun ziyarci Shasha

Daga WAKILIN MU Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu, ya ce Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta yinƙura domin mara wa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo baya wajen dawo da zaman lafiya a kasuwar Shasha da ke Ibadan, bayan hargitsin da ya auku a kasuwar cikin makon da ya gabata. Bagudu ya faɗi haka ne a Talatar da ta gabata, sa'ilin da yake magana da manema labarai yayin ziyarar gani da ido da shi da wasu takwararorinsa suka kai kasuwar. Tawagar gwamnonin da ta yi wannan ziyara ta ƙunshi Gwamna Bagudu na jihar Kebbi da Abdulahi Ganduje na jihar Kano da…
Read More
Okonjo-Iweala ta zama shugabar WTO

Okonjo-Iweala ta zama shugabar WTO

Daga AISHA ASAS Majalisar Ƙoli ta Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), ta tabbatar da Dr. Ngozi Okonjo-Iweala daga Nijeriya a matsayin Babbar Daraktar ƙungiyar. Da wannan, Okonjo-Iweala ta zama ta bakwai kenan daga jerin waɗanda suka riƙe wannan muƙami. Ranar 1 ga watan Maris ake sa ran Okonjo-Iweala za ta kama aiki, inda za ta kasance mace ta farko daga Nahiyar Afirka da ta taɓa ɗarewa kan muƙamin. Za ta riƙe wannan muƙami ne na tsawon shekaru huɗu masu zuwa, wato dai wa'adinta zai ƙare ne ya zuwa 31 ga Agustan 2025. A cewar Shugaban Majalisar ƙungiyar, David Walker daga…
Read More
Kamfanin BUA ya samu ribar bilyan N95 a 2020

Kamfanin BUA ya samu ribar bilyan N95 a 2020

Daga AISHA ASAS Kamfanin sarrafa siminti na BUA, ya bada sanarwar cewa ya tara kuɗaɗen shiga har naira bilyan N209 a 2020 inda ya ce ya samu ƙarin kashi 19 cikin 100 idan aka kwatanta da abin da ya tara 2019. Haka nan, kamfanin ya ce a bara ya samu ribar naira bilyan N95.4 wanda a cewarsa hakan ya ɗara ribar da ya samu a 2019 da kashi 16 cikin 100 inda ya samu naira bilyan N82.4. Duka waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun Shugaban Sashen Sadarwa na Kamfanin, Sunday Ogieva, wadda Manhaja ta…
Read More
Oyo: Makinde ya rufe kasuwar Shasha saboda ɓarkewar rikici

Oyo: Makinde ya rufe kasuwar Shasha saboda ɓarkewar rikici

Gwamman jihar Oyo, Engr. Seyi Makinde, ya bada umarnin rufe kasuwar Shasha da ke Ibadan har sai abin da Allah Ya yi biyo bayan ɓarkewar rikici a tsakanin 'yan kasuwan kasuwar. Kazalika, gwamnan ya sanya dokar taƙaita zirga-zirga a ciki da kewayen ƙaramar hukumar Akinyele sakamakon zaman ɗar-ɗar da jama'a ke yi a yankin da kasuwar take. Duka wannan ya faru ne a ranar Asabar, 13/02/2021. Sanarwar da ta fito daga ofishin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar, Mr. Taiwo Adisa, ta nuna Gwamna Makinde ya ɗauki wannan mataki ne domin lafar da ƙurar da hargitsin ya tayar. Sakataren…
Read More
Ɓata-gari sun far wa jami’an Kwastam a Ogun

Ɓata-gari sun far wa jami’an Kwastam a Ogun

Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a Jihar Ogun, ta ce wasu 'yan fasa-ƙwauri sun kai wa jami'anta hari a bakin aiki a Larabar da ta gabata inda aka yi musayar wuta wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar wani mazaunin ƙauyen Ohunbe mai suna Tunde Alabe. A cewar hukumar an yi arangamar ne a lokacin da jami'an kwastam suka yi ƙoƙarin daƙile fasa-ƙwaurin fetur zuwa ƙetare da masu harkar suka so yi. Ta ce ɓata-garin sun far wa jami'anta ne ɗauke da muggan makamai da suka haɗa da sanduna da bindigogi da dai makamantansu. Lamarin ya yi…
Read More