Kasuwanci

Kamfanonin MTN da Airtel sun samu lasisin gudanar aikin banki

Kamfanonin MTN da Airtel sun samu lasisin gudanar aikin banki

Daga AMINA YUSUF ALI Manyan kamfanonin sadarwar nan na MTN da Airtel sun samu lasisin tafiyar da harkokin banki da hada-hadar kuɗi a Nijeriya. Shi dai kamfanin MTN, wanda ya mamaye kaso 40 na kasuwar sadarwa a ƙasar, da kuma Airtel, wanda ya mamaye kaso 27, sun samu sahalewar Babban Bankin Nijeriya (CBN), domin su fara tafiyar da harkokin banki a faɗin ƙasar, kamar yadda jiga-jigan  kamfanonin sadarwar guda biyu suka bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata.  Kamfanonin sun bayyana hakan a wasu takardu mabanbanta da kamfanonin sadarwar suka aike wa da hukumar canji ta ƙasar Nijeriya.  Shi dai…
Read More
Gobara ta kashe rayuka a kasuwar Kubwa da ke Abuja

Gobara ta kashe rayuka a kasuwar Kubwa da ke Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Ana kyautata zaton wasu 'yan kasuwa sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar Maitama da ke Kubwa, ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja. A cewar wani shaidar gani da ido, gobarar ta fara ci ne misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Juma'a. Rahotanni sun nuna cewa, wutar ta fara ci ne daga wani shago da ke sayar da kalanzir a kasuwar. Rahoton ya ce, matar da ke sayar da kalanzir ɗin da yaranta na cikin waɗanda ake kyautata zaton sun, amma a samu damar tabbatar da hakan ba. Kuma…
Read More
kamfanin KEDCO ya tsawatar kan lalatawa da sace musu kayan aiki

kamfanin KEDCO ya tsawatar kan lalatawa da sace musu kayan aiki

Daga IBRAHIM HAMISU Mahukuntan kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na yankin Kano, wato KEDCO, ya yi kira ga ɗaukacin al'umma, musamman ma waɗanda suke lalata musu kayan aiki da jone-jonensu da su raba kansu da yin wannan aiki ba don komai ba ma, ko don haɗarin da ke tattare da yin haka gare su.  Kamfanin ya bayyana cewa, wannan kira da jan hankali ya biyo bayan wani abu da ya faru a kwanan nan inda wani mutum ya haɗu da ajalinsa sakamakon jan sa da wutar lantarkin ta yi, yayin da ya ke ƙoƙarin ta'annati a kan wasu wayoyin wuta…
Read More
Sanusi ya jaddada kira ga Buhari kan cire tallafin mai da lantarki

Sanusi ya jaddada kira ga Buhari kan cire tallafin mai da lantarki

Daga AMINA YUSUF ALI Mai Martaba Sarkin Kano na 14 kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Malam Muhammadu Sanusi II ya ƙara jaddada kiransa ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a kan ta janye tallafin man fetur da ta ke bayarwa a ƙasar. A cewar Sanusi II, ɗiban kuɗaɗe daga baitulmalin ƙasar da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ke yi yana karkatar da su a matsayin tallafin mai abu ne haramtacce, domin waɗannan kuɗaɗen an tanade su ne kuma mallakin ita Gwamnatin Tarayya ne da na jihohi da kuma ƙananan hukumomi, domin su yi wa al'ummar…
Read More
Bankin AfDB zai samar da guraben aiki miliyan 25 zuwa shekarar 2025

Bankin AfDB zai samar da guraben aiki miliyan 25 zuwa shekarar 2025

Daga AMINA YUSUF ALI Bankin cigaban Afirka  (AfDB) ya bayyaana cewa, yanzu haka Bankin yana da aniyar samar da guraben ayyukan yi guda miliyan 25, kafin nan kafin shekarar 2025, a Nijeriya.  Hukumar rukunin bankunan na ƙoƙarin tabbatar da hakan ne ta hanyar zuba hannayen jari masu gwaɓi a masana'antun fasahar zamani na ƙasar nan. Tare da haɗa hannu da wasu kamfanonin don samun guraben ayyuka barkatai a Nijeriya.  Wannan bayanai sun fito ne daga bakin shugaban rukunan AfDB, Dakta Akinwunmi Adesina a ranar Juma'ar da ta gabata. A yayin da yake gabatar da lakca a kan yadda shafukan yanar…
Read More
Kwamitin tsafta ya yi tir da rashin tsaftar kasuwar Tarauni a Kano

Kwamitin tsafta ya yi tir da rashin tsaftar kasuwar Tarauni a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Kwamitin duba-garin tsaftar muhalli na Jihar Kano ya yi Allah wadai da rashin tsaftar mayankar kasuwar Tarauni da ke yankin Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano.  Shugaban kwamitin, Dakta Kabiru Getso shi ya sanar da haka ga manema labarai bayan yin nazari a kan rahoton tsaftar muhalli da ake yi kowanne wata a Kano.  Dakta Getso, wanda shi ne kuma kwamishinan muhalli a jihar Kano, ya ƙara da cewa, abin takaici ne da juyayi da damuwa a game da yanayin da suka tarar da kasuwar ta Taraunin a ciki duk da yawan ziyarar da duba-garin suke…
Read More
Kotu ta umarci CBN ya sakar wa wasu kamfanoni asusunsu

Kotu ta umarci CBN ya sakar wa wasu kamfanoni asusunsu

Daga AMINA YUSUF ALI Kotun Ƙoli dake zamanta a Birnin Tarayyar Abuja a ƙarƙashin shugabancin Mai Shari'a Taiwo Taiwo ta umarci Babban Bankin Nijeriya, CBN da ya buɗe asusun ajiyar wasu kamfanoni da CBN ɗin ya daskarar da su. Domin a cewar kotun, ba a kan doka aka daskarar musu da asusun nasu ba.  A ranar 17 ga Agusta, 2021 ne dai Babban Bankin ya samu sahalewar wata kotu ba tare da zama ba a kan ta amince masa ya daskarar da asususun kamfanonin Rise Vest Technologies Limited, Bamboo Systems Technology Limited, Bamboo Systems Technology Limited OPNS, Chaka Technologies Limited,…
Read More
Bankunan China za su soma karɓar kuɗin Nijeriya

Bankunan China za su soma karɓar kuɗin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH A wani mataki na yauƙaƙa dangantaka da kuma haɓaka kasuwanci tsakanin China da Nijeriya, China ta ce bankunan ƙasar za su soma karɓar kuɗin Nijeriya, wato Naira. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Jakadan Ƙasar China a Nijeriya, Cui Jianchun kamar dai yadda mai bai wa Shugaban Ƙasa Mummadu Buhari shwara kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na facebook a ranar Alhamis. Cui Jianchun ya ce wannan mataki zai taimaka wajen bunƙasawa tare da sauƙaƙa gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin Nijeriya da China.
Read More
Bankin Access zai haɗe reshensa na ƙasar Zambiya da African Banking Corporation

Bankin Access zai haɗe reshensa na ƙasar Zambiya da African Banking Corporation

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai Bankin Access yana shirin haɗe reshenta na ƙasar  Zambiya da wani sabon bankin da ya mallaka watanni tara da suka wuce a can ƙasar Zambiya. Wato African  Banking Corporation, Zambiya. Bankin access shi ne bankin da ya fi kowanne banki a ƙasar nan ƙarfin kadara. Kuma ya samu damar mallakar wancan rukunin bankin na Zambiya watanni tara da suka gabata.  Wannan haɗakar kamar yadda jaridar premiumtimes ta rawaito, za ta ƙara haɓaka yawan bankunan Access ɗin a ƙasar Afirka ta Kudu har zuwa rassa guda 70 a ƙasar. Sannan zai ƙara wa…
Read More
Ba sai da wayar Andiroi ‘yan Nijeriya za su iya hada-hadar eNaira ba – CBN

Ba sai da wayar Andiroi ‘yan Nijeriya za su iya hada-hadar eNaira ba – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya, CBN ya bayyana cewa, ba fa sai da wayar andiroyi ko da yanar gizo 'yan Najeriya za su iya yin hada-hadar kuɗi na eNaira ba. Ita dai eNaira kamar yadda Babban Bankin ya bayyana cewa, shi ma tsari ne kamar sauran tsarin hada-hadar kuɗi ta yanar gizo ko manhajojin hada-hadar kuɗi na kan waya da muke da su da ma.  Inda ya ƙara da cewa, tsarin zai ƙara wa 'yan Najeriya sauƙin hada-hadar banki tare da faɗaɗa shi. Domin za a dinga hada-hadar ba tare da sayen data don shiga yanar gizo ba.…
Read More