Daga AMINA YUSUF ALI
Bankin cigaban Afirka (AfDB) ya bayyaana cewa, yanzu haka Bankin yana da aniyar samar da guraben ayyukan yi guda miliyan 25, kafin nan kafin shekarar 2025, a Nijeriya.
Hukumar rukunin bankunan na ƙoƙarin tabbatar da hakan ne ta hanyar zuba hannayen jari masu gwaɓi a masana’antun fasahar zamani na ƙasar nan. Tare da haɗa hannu da wasu kamfanonin don samun guraben ayyuka barkatai a Nijeriya.
Wannan bayanai sun fito ne daga bakin shugaban rukunan AfDB, Dakta Akinwunmi Adesina a ranar Juma’ar da ta gabata. A yayin da yake gabatar da lakca a kan yadda shafukan yanar gizo da tsaron ƙasa da kuma sauye-sauyen rayuwa da za su iya kawo daidaito a Afirka. An gudanar da taron a jihar Legas.
A cewar sa, Nijeriya tana da damarmaki da yawa waɗanda ƙasashen Duniya suke da buƙatar su ma su shigo a dama da su, wajen zuba jari da kasuwanci.
Ya ƙara da cewa, a yanzu haka, AfDB ya shirya tsaf, don tallafa wa Nijeriya. Inda nan ba da daɗewa ba, za su zuba hannun jarin Dala miliyan ɗari biyar a sassan fasahar zamani da kasuwanci a ƙasar.
Wanda suke sa ran shigowar wasu ƙasashen domin su ma su ba da tasu gudunmowsr don a haɗa gwiwa a cimma manufar da aka nufa.