Sanusi ya jaddada kira ga Buhari kan cire tallafin mai da lantarki

Daga AMINA YUSUF ALI

Mai Martaba Sarkin Kano na 14 kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Malam Muhammadu Sanusi II ya ƙara jaddada kiransa ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a kan ta janye tallafin man fetur da ta ke bayarwa a ƙasar.

A cewar Sanusi II, ɗiban kuɗaɗe daga baitulmalin ƙasar da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ke yi yana karkatar da su a matsayin tallafin mai abu ne haramtacce, domin waɗannan kuɗaɗen an tanade su ne kuma mallakin ita Gwamnatin Tarayya ne da na jihohi da kuma ƙananan hukumomi, domin su yi wa al’ummar ƙasa aiki da su. Ya ce, don haka da daidai ba ne yadda Gwamnatin Tarayya ta ke ɗaukar kuɗaɗen tana yin zarafinta ita kaɗai ba.  

Tsohon Sarkin ya bayyana hakan ne a Talatar da ta gabata, 26 ga Oktaba, 2021. A yayin da yake jawabi a taron tattalin arzikin Najeriya wanda aka yi a Abuja. 

Sunusi ya ƙara da cewa, wannan kuɗi mallakar asusun gwamnatin tarayya ne ba mallakin gwamnatin tarayyar ba. Don haka, Gwamnatin Tarayyar ba ta da hurumi a kundin tsarin mulkin ƙasar nan da ya ba ta dama don ta karkatar da waɗancan kuɗaɗen don yin tallafin man.

Don haka a cewar sa, ya kamata Buhari ya gaggauta cire tallafin man domin hakan zai iya kai wa ga dagulewar al’amura domin hakan ya ci karo da dokar kundin tsarin mulkin ƙasar nan. 

Inda ya nuna juyayinsa a kan yadda farashin safarar man fetur ɗin ya tashi lokaci guda har ma ya ninka kuɗinsa na asali. 

Wannan batu na Sunusi, ba wannan ne karo na farko da ya fara faɗar sa ba. Ya taɓa yin makamancin wannan furucin a baya. Kuma abin ya ta da ƙura matuƙa. 

Da take mayar da martani a kan kiran da tsohon sarkin yake yi wa Gwamnatin Tarayya, Ministar kuɗi  Zainab Ahmed, ta ce ba gudu ba ja da baya, gwamnatin za ta cigaba da biyan kuɗin tallafin man har i zuwa ƙarshen wa’adin mulkin Buhari.