kamfanin KEDCO ya tsawatar kan lalatawa da sace musu kayan aiki

Daga IBRAHIM HAMISU

Mahukuntan kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na yankin Kano, wato KEDCO, ya yi kira ga ɗaukacin al’umma, musamman ma waɗanda suke lalata musu kayan aiki da jone-jonensu da su raba kansu da yin wannan aiki ba don komai ba ma, ko don haɗarin da ke tattare da yin haka gare su. 

Kamfanin ya bayyana cewa, wannan kira da jan hankali ya biyo bayan wani abu da ya faru a kwanan nan inda wani mutum ya haɗu da ajalinsa sakamakon jan sa da wutar lantarkin ta yi, yayin da ya ke ƙoƙarin ta’annati a kan wasu wayoyin wuta na hukumar KEDCO, inda ya taki rashin sa’a aka kawo wuta a yayin da yake tsaka da aika-aikar da yake ƙoƙarin yi ta satar wayoyin wutar.

Da faruwar hakan abokan aikinsa da suke tare, suka ranta a na kare suka bar gawar abokin nasu.

Da wannan ne hukumar ta ce tana kira ga al’umma da su nesanta kansu da duk wani ta’adi da suka san zai sanya rayuwarsu da ta al’umma a cikin haɗari, inda suka ƙara da cewa, ko da wani abu ne da ya shafi wutar lantarki ya samu matsala, to kada ma al’umma su yi gaban kansu da yunƙurin gyarawa.

Gara su garzaya i zuwa ofishin KEDCO ma fi kusa da su don a gyara musu. Wato dai kada su sake ko da wasa su staɓa wayoyi ko jone-jonen da KEDCO ta yi domin tsaron lafiyarsu da ta sauran al’umma.

Daga ƙarshe, suka kuma yi ro}o ga al’umma da su sanar da duk wani yunƙuri da wasu suke yi don lalata kayan aikin KEDCO ɗin ko kuma idan an samu matsalar jone-jonen wutar lantarki, a sanar wa ofishin KEDCO, domin a gyara musu kai-tsaye, ba tare da ɓata lokaci ba.