Gobara ta kashe rayuka a kasuwar Kubwa da ke Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Ana kyautata zaton wasu ‘yan kasuwa sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar Maitama da ke Kubwa, ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.

A cewar wani shaidar gani da ido, gobarar ta fara ci ne misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa, wutar ta fara ci ne daga wani shago da ke sayar da kalanzir a kasuwar.

Rahoton ya ce, matar da ke sayar da kalanzir ɗin da yaranta na cikin waɗanda ake kyautata zaton sun, amma a samu damar tabbatar da hakan ba.

Kuma ana kyautata zaton cewa, aƙalla mutane uku sun rasu yayin da wasu da dama suka jikkata.

Da aka tuntuɓe ta, muqadashin shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Abuja, Florence Wenegieme ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ƙara da cewa, ’yan daba masu neman ɗibar ganima sun mamaye wurin sun hana jami’an kwana-kwana su wuce su yi aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *