Kwamitin tsafta ya yi tir da rashin tsaftar kasuwar Tarauni a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI

Kwamitin duba-garin tsaftar muhalli na Jihar Kano ya yi Allah wadai da rashin tsaftar mayankar kasuwar Tarauni da ke yankin Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. 

Shugaban kwamitin, Dakta Kabiru Getso shi ya sanar da haka ga manema labarai bayan yin nazari a kan rahoton tsaftar muhalli da ake yi kowanne wata a Kano. 

Dakta Getso, wanda shi ne kuma kwamishinan muhalli a jihar Kano, ya ƙara da cewa, abin takaici ne da juyayi da damuwa a game da yanayin da suka tarar da kasuwar ta Taraunin a ciki duk da yawan ziyarar da duba-garin suke zuwa yi don tabbatar da tsaftace muhalli a kowanne wata.

A cewar sa, wannan abin zai tursasa wa kwamitin nasu ya binciki waɗanda suke da alhakin kula da duba tsaftar ɓangaren ƙaramar hukumar Taraunin. 

Hakazalika, Dakta Getso ya bayyana cewa, yanzu haka kwamitin ya ba wa mahukuntan kasuwar ta Tarauni wa’adin sati biyu domin su tabbatar da sun tsaftace mayankar. Inda ya ce, kwamitin nasu zai ba da gudunmowa ga ‘yan kasuwar domin su tsaftace ta. Sannan zai sa ido don ganin an tabbatar da hakan. 

Shi dai tsarin duba-garin tsaftar muhalli abu ne da ake yinsa kowacce Asabar ɗin ƙarshen wata a Jahar Kano don tabbatar da tsaftar muhalli a jihar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *