Kotu ta umarci CBN ya sakar wa wasu kamfanoni asusunsu

Daga AMINA YUSUF ALI

Kotun Ƙoli dake zamanta a Birnin Tarayyar Abuja a ƙarƙashin shugabancin Mai Shari’a Taiwo Taiwo ta umarci Babban Bankin Nijeriya, CBN da ya buɗe asusun ajiyar wasu kamfanoni da CBN ɗin ya daskarar da su. Domin a cewar kotun, ba a kan doka aka daskarar musu da asusun nasu ba. 

A ranar 17 ga Agusta, 2021 ne dai Babban Bankin ya samu sahalewar wata kotu ba tare da zama ba a kan ta amince masa ya daskarar da asususun kamfanonin Rise Vest Technologies Limited, Bamboo Systems Technology Limited, Bamboo Systems Technology Limited OPNS, Chaka Technologies Limited, CTL/Business Expenses, da kuma Trove Technologies Limited na tsahon kwanaki 180 a kan laifin karya dokar canjin kuɗi da CBN ɗin yake zargin kamfanonin da shi. 

Majiyarmu ta bayyana cewa, bayan binciken da kotun ta yi ne aka tabbatar da cewa, babu wata sahihiyar hujja da take tabbatar da cewa, waɗancan kamfanonin sun aikata abinda CBN ɗin yake zargin su. Hasali ma sun kasance masu bin dokar Bankin sau da ƙafa. 

Da yake gudanar da hukunci a kan ƙarar, Mai Shari’a Taiwo ya bayyana cewa, har yanzu dai CBN ya kasa zuwar wa da kotu wata sahihiyar hujjar da take nuna cewa, dokar Nijeriya ta haramta ta’ammali da kiriftokaransi (cryptocurrency) a ƙasar nan. Kuma a cewar sa, dokar CBN ɗin mai lamba BSD/DIR/PUB/LAB/014/001 ta 5 ga watan Fabrairu, 2021, ba cikakkiyar doka ba ce. Kuma Bankin ba shi da hurumin zartar da wani hukunci wanda ba ya rubuce a kundin tsarin mulki na ƙasar Nijeriya. 

Mai Shari’ar ya ƙara da cewa, haƙiƙanin gaskiya CBN yana da hurumin gudanar da bincike a kan dukkan masu karya doka a kan harkar kuɗi, amma ba ta da hurumin rufe asusu ba bisa ƙa’ida ba. 

Da waɗancan hujjojin Mai Shari’ar ya ce ya kore wancan hukuncin da Bankin ya yanke kan waɗancan Kamfanoni a ranar 17 ga Agusta, 2021. Kuma ya ba da umarnin Bankin ya sakar musu asusun nasu da ya garƙame.