Kasuwanci

Da ɗumi-ɗumi: Jirgin saman Nijeriya zai soma aiki a Afrilun 2022

Da ɗumi-ɗumi: Jirgin saman Nijeriya zai soma aiki a Afrilun 2022

Daga BASHIR ISAH Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Hadi Sirika, ya bayyana cewa ana sa ran jirgin saman Nigeria Air zai soma aiki ya zuwa Afrilun 2022. Sirika ya bayyana haka ne sa'ilin da yake zantawa da wakilan jaridu a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zaratarwa a ranar Laraba. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, shi ne wanda ya jagoranci taron na ranar Laraba. A cewar Sirika, zirga-zirgar jirgin a cikin ƙasa zai kasance ne a ƙarƙashin kulawar wani kamfani inda gwamnati ke da hannun jari na kashi 5% a ciki. Ya ci gaba da cewa, 'yan…
Read More
Gobara ta ƙone shaguna 41 a Kasuwar Kurmi da ke Kano

Gobara ta ƙone shaguna 41 a Kasuwar Kurmi da ke Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da ƙonewar shaguna 41 a ɓangaren ƴan Littafi da ke ƙasuwar kurmi a ƙaramar hukumar birni ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda shi ne Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukumar ne ya tabbatar da gobarar a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a yau Litinin. Abdullahi ya ce hukumar ta ƙarɓi rahoton gobarar ne ta wayar salula daga wani Malam Bala Nasidi da misalin ƙarfe 10:58 cewa akwai gobara a ƴan littattafai kasuwar. "Muna karɓar rahoton, bamu yi ƙasa a gwiwa ba mu ka garzaya wajen…
Read More
Sai nan da 2025 za a kuɓutar da ‘yan Nijeriya miliyan 25 daga ƙangin talauci – Osinbajo

Sai nan da 2025 za a kuɓutar da ‘yan Nijeriya miliyan 25 daga ƙangin talauci – Osinbajo

Daga Amina Yusuf Ali Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, Nijeriya ta gama tanadinta tun daga wannan shekarar ta 2021 domin tabbatar da cewa an kuɓutar da 'yan Nijeriya mutum miliyan 25 daga ƙangin talauci sannan kuma za a kange wasu miliyan goma daga afkawa ƙangin talaucin. Osinbajo wanda Sakataren Gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ya wakilta ne ya bayyana hakan a taron tattalin arziki wanda NiDCOM ta shirya. Inda ya ƙara da cewa, tallalin arzikin Nijeriya ya ƙara bunƙasa a yanzu. Sannan kuma sanadiyyar sabbin abokan hulɗar da Nijeriya ta ƙara samu sakamakon annobar Covid19, za…
Read More
FIRS ta tara Naira tiriliyan 4.2 a cikin wata tara kacal

FIRS ta tara Naira tiriliyan 4.2 a cikin wata tara kacal

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tattara haraji ta tarayyar Njeriya (FIRS), ta bayyana cewa, ta tattara haraji da ya kai Naira tirilian hu]u da biliyan biyu a tsakanin watanni tara kacal. Wato tsakanin watan Janairu zuwa watan Satumbar shekaran nan ta 2021. Shugaban zartarwa na hukumar tattara harajin, ta FIRS, Mista Mohammad Nami shi ya bayyana haka a yayin taron ranar FIRS ta musamman wato ranar baje-kolin kasuwancin ƙasa da ƙasa wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Jahar legas.  Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa, Mohammad Nami ya ce, hukumar FIRS ta yi ƙoƙari wajen cimma tattara waɗancan maƙudan…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da manhajojin ba da rance

Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da manhajojin ba da rance

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta gurfanar da kamfanonin da suke tafiyar da manhajojin ba da rance a yanar gizo saboda laifin tozarta bayanan sirri na al'umma. Hukumomin EFCC da  NITDA da kuma FCCPC suka bayyana cewa, a shirye suke don gurfanar da manyan kamfanonin rance kamar NowCash da Sokoloan da kuma 9credit saboda zargin suna fallasar da sirrikan mutane a yanar gizo.  Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin wani jawabin manema labarai da hukumar fasahar samar da bayanai ta ƙasa, NITDA ta wallafa a shafinta na Fesbuk.  Hukumar ta bayyana cewa, a yanzu…
Read More
Tsadar dakon kaya daga Chana zuwa Legas ya fi sauƙi kan daga Legas zuwa Kano – Abdussamad

Tsadar dakon kaya daga Chana zuwa Legas ya fi sauƙi kan daga Legas zuwa Kano – Abdussamad

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdussamad Rabi'u ya bayyana cewa, safarar kaya daga Chana zuwa Legas ya fi sauƙi matuƙa da araha a kan daga Legas zuwa Kano da ke arewacin Nijeriya.  Abdussamad ya bayyana haka ne a yayin da ya ke yin tsokaci a game da yadda za a sauƙaƙa harkokin sufuri a Nijeriya, musamman ma ɓangaren jirgin ƙasa. Ya yi wannan jawabi ne a garin Faris na ƙasar Faransa.  Inda ya ƙara da cewa, da Nijeriya za ta dage a kan inganta hanyoyin sufuri musamman na jirginƙasa, da ba ƙaramin alfanu hakan zai samar ba…
Read More
Dalilin da ya sa Coca-cola ya maka Pop-cola a kotu

Dalilin da ya sa Coca-cola ya maka Pop-cola a kotu

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Coca-cola ya maka takwaransa na Mamuda Beverages Nigeria limited mai sarrafa lemon kwalbar nan na Pop-cola, a Babbar Kotun Kano kan zargin satar alamar kasuwancinsa. Kano Focus ta ruwaito cewa, kamfanin Mamuda Beverages Nigeria limited ya ƙaddamar da lemon kwalba na Pop-cola ne a watan Yunin da ya gabata. Coca-cola na zargin kamfanin Mamuda Beverages da kwaikwayon zane wajen tsara alamarsa ta kasuwanci a jikin kwalba wanda ya ce zanen sak yake da nasa wanda hakan na haifar da ruɗani ga kwastomominsa inda wasunsu kan ɗauki Pop-cola a matsayin Coca-cola. Bayan sauraren lauyoyin duka ɓangarorin biyu,…
Read More
An ci tarar GT Bank da bankuna huɗu kan haramtacciyar harƙallar kuɗi

An ci tarar GT Bank da bankuna huɗu kan haramtacciyar harƙallar kuɗi

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma hukumar kula da hada-hadar hannun jari ta ƙasa (SEC) sun ci tarar wasu bankuna guda biyar a kan laifuffuka har guda ashirin da suke da alaƙa da haramtacciyar harƙallar kuɗi da kuma karya dokar canjin kuɗi, inda aka caji kamfanonin jimillar tarar Naira biliyan guda da kusan rabi.  Bankunan da abin ya shafa su ne: Guaranty Trust Holding Company Plc, United Bank for Africa Plc, Access Bank Plc, Stanbic IBTC Holdings Plc da kuma Fidelity Bank Plc. Daga cikin bankunan, Bankin GT Holding shi ya fi amsar tara ma fi…
Read More
Kamfanin NNPC ya wanke kansa bisa ƙarancin fetur da ya game Nijeriya

Kamfanin NNPC ya wanke kansa bisa ƙarancin fetur da ya game Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI A ƙarshen makon da ya gabata ne aka wayi gari da dogayen layuka a gidajen mai, a wasu jihohi a Nijeriya. Hakan ba ya rasa nasaba da irin matsanancin ƙarancin man fetur, da dangoginsa a ƙasar. Inda wasu gidajen man duk an kulle su, wasu kuma ba sa buɗewa sosai.  Matsalar man fetur ɗin ta zo ne bayan wasu zantuka da ake yayatawa da ake kyautata zaton daga bakin dillalan man fetur ɗin suka fito. Inda aka bayyana cewa, za a samu ƙarin farashin man. Ita a nata ɓangaren, hukumar kula da man fetur NNPC, ta…
Read More
Haƙar ma’adanai: Najeriya ta yi tayi mai maiƙo ga masu zuba jari

Haƙar ma’adanai: Najeriya ta yi tayi mai maiƙo ga masu zuba jari

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga al'umma da su zo su zuba jari a harkar haƙar ma'adanai a ƙasar. Inda Gwamnatin ta yi tayi maiƙo ga dukkan waɗanda za su zuba jari a harkar. Wato Gwamnatin ta ce za ta mallaka musu dukkan ma'adanan ko albarkatun ƙasar da suka haƙo ba tare da ta karɓi ko tsinke ba. Sannan za ta yafe musu haraji na tsawon lokaci. Wannan tayi ya haɗa da dukkan masu sha'awar zuba jari na gida Nijeriya da kuma na ƙasashen ƙetare.  Ministan masana'antar tama da ƙarafa, Olamilekan Adegbite, shi ya bayyana hakan…
Read More