Dalilin da ya sa Coca-cola ya maka Pop-cola a kotu

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin Coca-cola ya maka takwaransa na Mamuda Beverages Nigeria limited mai sarrafa lemon kwalbar nan na Pop-cola, a Babbar Kotun Kano kan zargin satar alamar kasuwancinsa.

Kano Focus ta ruwaito cewa, kamfanin Mamuda Beverages Nigeria limited ya ƙaddamar da lemon kwalba na Pop-cola ne a watan Yunin da ya gabata.

Coca-cola na zargin kamfanin Mamuda Beverages da kwaikwayon zane wajen tsara alamarsa ta kasuwanci a jikin kwalba wanda ya ce zanen sak yake da nasa wanda hakan na haifar da ruɗani ga kwastomominsa inda wasunsu kan ɗauki Pop-cola a matsayin Coca-cola.

Bayan sauraren lauyoyin duka ɓangarorin biyu, Alƙalin kotun, Muhammad Nasir-Yunusa ya ɗage shari’ar zuwa 11 ga Disamba mai zuwa don ci gaba da shari’a.