Gobe za a ƙaddamar da Ƙungiyar Haɓaka Harshen Hausa a Neja

Daga BASHIR ISAH

Gobe Labara idan Allah Ya kai mu, ake sa ran gudanar da taron ƙaddamar da Ƙungiyar Haɓɓaka Harshen Hausa ta Ƙasa reshen Jihar Neja domin ci gaba da bunƙasa harshen Hausa yadda ya kamata.

Taron wanda za a soma shi daga kan ƙarfe 10 na safe, zai gudana ne a Cibiyar Nazarin Harkokin Shari’a da Gudanarwa ta Fati Lami Abubakar (FLAILAS) da ke yankin Kpakungu a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Manyan baƙin da ake sa ran su halarci taron sun haɗa da: Mai Martaba Sarkin Minna, Alh. (Dr.) Umaru Farouq Bahago da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza daga Jami’ar Usmanu Ɗanfodio, Sakkwato, da Farfesa Muhammad Yakubu Auna, shugaban C.O.E Minna.

Sauran su ne, Dr Admu Ibrahim Malumfashi daga ABU Zaria, Dr. Muhammad Aliyu Busa, shugaban FLAILAS da dai sauransu.

Kazalika, ana sa ran wasu masana harshen Hausa su gabatar da muƙalu daban-daban kan batutuwan da suka shafi harshen.

Da wannan ne kwamitin shirye-shiyen taron, ya ce yana gayyatar jama’a na kusa da nesa da su halarci wannan taro saboda muhimmancinsa da kuma kafa tarihi.